In da rai, da rabo: Daga mai gyaran takalmi zuwa shugaban jami'a

In da rai, da rabo: Daga mai gyaran takalmi zuwa shugaban jami'a

Labarin Farfesa Andrew Haruna na daya daga cikin labaran mutanen da suka yi nasara ta hanyar jajircewa, aiki tukuru da kuma rashin yanke tsammani. Wadannan abubuwan kuwa na iya sa mutum ya kai kololuwar daukaka.

Farfesa Haruna shine shugaban jami’ar tarayya da ke Gashua, jihar Yobe. A farkon rayuwarsa, ya dukufa ne yin kananan aiyuka don samun mafita. Tun kuwa yana karami yake son karatu tare da burin zama mai ilimi. Hakan kuwa ne yas ya fara zuwa makaranta duk da iyayenshi bas u da kudin kaishi.

An haifeshi a 1957 akauyen Gar da ke karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi. Tun yana yaro, Haruna ya dukufa wajen noma, sayar da itace da kosai tare da sauran kananan aiyuka don samun kudin da zai taimaki iyayensa wadanda bas u iya biya mishi kudin makaranata ba, jaraidar Sun News ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Yadda bindigar shaida ta harbe lauya a kotu

Duk da kuwa suna goyon bayan burin dannasu, babu abinda suke iyawa sai nuna mishi soyayya tare da kula. Hakan kuwa yas Haruna yake yin duk yadda zai yi don biyan kudin makarantarsa.

Ya yi karatunsa na firamare a Gar daga 1964 zuwa 1970. Ya koma kwalejin gwamnati ta Maiduguri daga 1971 zuwa 1975. Ba biyan kudin makaranta kadai ne a lokacin ya zamo kalubale ga Haruna ba, har da nisan makarantarsu daga gida. Makarantar na da nisan kilomita 600 daga gidansu.

Bayan kammala karatun sakandire, ya zauna a Maiduguri inda ya fara hada takalma don samun kudin cigaba da karatu zuwa jami’a.

Ya kan yi wa ma’aikata kananan aiyuka duk don tara taro da sisi. A hakan ne ya hadu da wata budurwa da ta taimaka masa ya cigaba da karatunsa.

A 1982 ne ya samu aiki a jami’ar Maiduguri. Daga 1083 zuwa 1990 ne ya garzaya jami’ar landan inda ya karo karatu. A shekarar 2016, an zabi Haruna a matsayi shugaban jami’ar Maiduguri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel