Abinda Buhari ya fadi min a kan Yari - Sanata Yarima

Abinda Buhari ya fadi min a kan Yari - Sanata Yarima

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yarima ya yi bayanin abinda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da akan yadda tsohon gwamna Abdulazeez Yari ya kawo dan takararsa a zaben 2019.

Yarima, wanda ya tattauna da wani gidan rediyo da ke Gusau, Zamfara, ya ce ya hadu da Shugaba Buhari kafin zaben.

Yace, a lokacin da shugaban kasar ke bayyana matsayarsa a kan lamarin, ya ce "mun ji abinda Yari ya ke yi kuma bamu amince ba. Doka ce dole a yi zaben fidda gwani don tabbatar da zabin mutane."

Ya kara da cewa, "bayan haduwata da Buhari sai Oshiomhole ya kirani. Ya sanar dani 'Ina fada da Yari saboda shirinsa na saka dan takararsa. Na ce ba zamu amince ba amma ya cigaba da abinda yake so.' Na sanar da Oshiomhole zan samu Yari mu tattauna, kada ya damu."

DUBA WANNAN: Jama'a sun banka wa wani mutum da ake zargi da satar babur

"Na hadu da Yari kuma mun yi maganar. A take ya fadamin cewa, shugaban jam'iyyar na kasa bai isa ya hanashi abinda ya so yi ba. A take na sanar dashi matsayar Buhari a kan hakan. Sai yace, Kada ka sako shugaba Buhari cikin wannan maganar. Buhari bashi da hannu a wannan maganar, Oshiomhole ne." in ji Yarima.

Yarima ya bayyana yadda ya janye tare da fita harkar. Domin kuwa Yari ya ce, ya fita daga zancen amma in amfaninsa ya taso za a neme shi.

"Lokacin da Buhari ya zo kamfen Gusau, ya ce ba zai daga hannun wani dan takara ba kuma ya sanar da masu ruwa da tsaki matsayarsa. A nan na kara jawo hankalin Yari a kan abinda Buhari ya ce a taron masu ruwa da tsakin jam'iyyar lokacin da ya zo kamfen," inji Yarima.

A halin yanzu, Sanata Sani Yarima ya ce ba zai kara takarar wata kujera ta jihar ba, amma mutanensa sun jawo hankalinsa da ya fito takarar shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel