Zaman lafiya da kwanciyar hankali sun samu a Najeriya – Sufetan Yansanda

Zaman lafiya da kwanciyar hankali sun samu a Najeriya – Sufetan Yansanda

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammad Adamu ya bayyana cewa an cigaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali daidai gwargwado a Najeriya a cikin yan watannin karshen shekarar nan.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito IG ya bayyana haka ne bayan fitowa daga wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi da manyan hafsoshin hukumomin tsaron Najeriya a ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba a fadar gwamnati.

KU KARANTA: EFCC ta kama kansila da ya yi damfarar naira miliyan 2.3 a Kaduna

IG Muhammad ya bayyana cewa a yayin zamansu da Buhari, sun yi nazari a kan yanayin tsaron da aka samu a Najeriya, sa’annan sun tattauna a kan hanyoyin da suka dace a bi wajen inganta tsaro a dukkanin sassan kasar.

“Taron ya yi nazari a kan halin tsaro da ake ciki a Najeriya, inda muka tabbatar da cewa akwai tsaro iya gwargado, hare haren yan bindiga ya ragu, haka zalika satar mutane maya ragu, kamar yadda kuka sani inda matsalar satar mutane ya fi shafa shi ne Zamfara, Katsina da Kaduna, a yanzu komai ya lafa.

“Game da batun yaki da ta’addanci kuwa, ana samun galaba a kansu a kullum a yankin Arewa maso gabas, sa’annan wasu yan ta’adda da dama suna mika wuya ga gwamnati, kuma suna mika makamansu, don haka an bamu kwarin gwiwar mu cigaba da aikinmu.

“Duk wadannan nasarori da muka samu mun same su ne a dalilin hadin kai da jama’a suke bamu, da kuma kafafen watsa labaru, musamman duba da yadda ku ke tsage bayani a kan matsalar tsaro, kuma mabiyanku suna gamsuwa daku.

“Sa’annan yan siyasa da mafarauta suna aiki damu tare da sauran masu ruwa da tsaki, don haka an bamu kwarin gwiwar mu cigaba da aiki tare da wadannan rukunin jama’a domin samun bayanai daga garesu.” Inji shi.

Dangane da rikicin da aka samu a yayin zaben gwamna a jahohin Bayelsa da Kogi, Muhammad yace sun yi kame, kuma Yansandan da ake zargi sun kai hare hare a ranar zaben Yansanda ne na bogi ba na gaskiya ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel