Yadda bindigar shaida ta harbe lauya a kotu

Yadda bindigar shaida ta harbe lauya a kotu

- Jami'an 'yan sandan kasar Afirka ta Kudu sun bayyana yadda wata lauya ta gamu da ajalinta a dakin kotu

- Kunamar bindiga ta dana kanta ne dai-dai lokacin da aka gabatar da ita a matsayin shaida gaban alkali

- Jami'an 'yan sandan sun ce suna gudanar da bincike kan mutuwar Miss Ferreira-Watt a matsayin kisa ba da gangan ba

Jami'an 'yan sanda a kasar Afirka ta Kudu sun bayyana yadda wata lauya ta gamu da ajalinta. Lauyar ta mutu har lahira ne a lokacin da harsashi bisa kuskure ya kufce daga bindigar da aka kawo kotu don kafa shaida da ita.

Lamarin ya faru ne a yankin Kwazulu Natal na kasar Afirka ta Kudun.

Lauyar mai suna Adelaide Ferreira- Watt ta hadu da ajalinta ne jim kadan bayan alburushin bindigar da ya kufce, ya sameta a kwankwaso.

DUBA WANNAN: 'Yan majalisa sun lalata tiriliyan daya da sunan aikin mazabu - Buhari

Kunamar bindigar ta dana kanta ne dai-dai lokacin da aka gabatar da ita a matsayin shaida gaban alkali a kan fashi da makami da aka yi a wani gida.

Jami'an 'yan sandan sun ce suna gudanar da bincike kan mutuwar Miss Ferreira-Watt a matsayin kisa ba da gangan ba.

Sun kara da tabbatar da cewa za su yi binciken dalilin da yasa aka kawo bindigar cikin kotun bayan an san da harsashi a cikinta. Sun ce hakan ya sabawa doka.

A wani labari da jaridar Legit.ng ta ruwaito a kwanakin baya, an ji yadda wani alkali ya harbi kansa a cikin dakin kotu bayan ya gama shari'a.

A gaban jama'ar da ke kotun ya tashi tsaye tare da bayyana musu cewa, ya gaji da zirga-zirgar duniyar nan. Ya juya musu baya tare da fito da karamar bindiga inda a take ya harbi kansa a kirji.

Tuni dai aka kwashi alkalin magashiyyan zuwa wani asibiti inda ya samu taimakon gaggawa daga ma'aikatan lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel