Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerun 'yan majalisu guda biyu a jihar Kaduna ta ce sai an sake sabon zabe

Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerun 'yan majalisu guda biyu a jihar Kaduna ta ce sai an sake sabon zabe

- Yanzun nan wata kotun daukaka kara dake zamanta a jihar Kaduna ta kwace kujerun wasu 'yan majalisun jihar Kaduna guda biyu

- Kotun ta kuma umarci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ta sake gabatar da sabon zabe a mazabun Sanga da Kagarko

- Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan abokanan hamayyar wadanda suka lashe zaben sun kalubalance su a kotun

A jiya Talata ne kotun daukaka kara dake jihar Kaduna, ta tsige wasu 'yan majalisar jihar guda biyu.

Kotun ta umarci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ta sake gabatar da zabe domin a tabbatar da 'yan majalisun da zasu wakilci mazabun Kagarko da Sanga.

A Kagarko kotun daukaka karar ta bukaci a sake gabatar da zabe a rumfunan zabe guda 22 a cikin mazabu biyu na yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bayyana cewa dan takarar majalisar jiha a jam'iyyar APC Mr. Nuhu Shadalafiya shine ya kalubalanci abokin takarar shi Mr. Morondia Tanko na jam'iyyar PDP wanda ya lashe zaben a ranar 9 ga watan Afrilun nan da ya gabata.

Kotun zaben ta bukaci a sake gabatar da sabon zabe a rumfunan zabe guda 22, amma shi kuma Tanko na jam'iyyar PDP ya bukaci kotun daukaka kara da ta dakatar da wannan umarni na kotun zabe ta bashi kujerar shi kamar yadda hukumar zabe ta kasa ta bayyana shi a matsayin wanda yayi nasara.

KU KARANTA: Ba wani abu bane dan jaruma tayi aure an saketa ta sake dawowa harkar fim - In ji Ummi Duniyar Nan

Yanzu haka dai kotun daukaka karar tayi watsi da wannan roko na Tanko ta kuma umarci hukumar zabe ta kasa da ta kara gabatar da sabon zabe a wadannan mazabun.

Lauyan Shadalafiya, Mr. Ussy Edikhiola ya bayyana cewa sunji dadi sosai akan hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke.

Hakazalika kotun daukaka karar ta kara bada umarnin sake zabe a mazabar Sanga wacce Mrs. Comfort Amwe ta jam'iyyar PDP ta samu nasara a kai.

Amwe ita ce kadai mace a cikin 'yan majalisar jihar ta Kaduna. Sai dai ta samu matsala bayan Alhaji Gambo Danga na jam'iyyar APC ya kalubalanci nasarar ta a kotun sauraron kararrakin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel