Kogi: 'Yan sanda sun fadi dalilin da yasa aka kashe shugaban mata na PDP a gidanta

Kogi: 'Yan sanda sun fadi dalilin da yasa aka kashe shugaban mata na PDP a gidanta

- 'Yan sanda sunyi karin haske game da mutuwar shugaban mata na yakin zabe na jam'iyyar PDP a jihar Kogi

- Wasu fusatattun matasa da ake zargin 'yan jam'iyyar APC ne suka bankawa gidan ta wuta kuma suka hana a ceto ta

- Binciken da 'yan sandan su kayi ya nuna cewa ramuwar gayya ne matasan suka yi don wani dan uwar matan ya kashe wani dan APC

Mai magana da yawun 'yan sanda a jihar Kogi, DSP Aya Williams ya tabbatarwa da kone shugaban yakin neman zabe na mata na jam'iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) na jihar Kogi, Misis Acheju Abuh da wasu 'yan daba da ake zargin 'yan jam'iyyar APC ne suka aikata a Ochadamu na karamar hukumar Ofu.

Ga sanarwar da 'yan sandan suka fitar kamar yadda Linda Ikeji Blog ya ruwaito.

Kisa da wuta da hadin baki:

"A ranar 18/11/2019 misalin karfe 4 da minti 30 na yamma, wani Musa Etu na garin Ochadamu, a karamar hukumar Ofu ya shigar da rahoto a caji ofis na cewa a misalin karfe 10 da rabi da safen ranar cewa an samu rashin jituwa tsakanin wani Awolu Zekeri dan shekaru 35 kuma dan jam'iyyar APC da wani Gowon Simeon dan jam'iyyar PDP duk mazauna Ochadamu.

"Sakamakon hakan Gowon Simeon ya dabawa Awolu Zekeri wuka a cinyarsa. Ya mutu a hanyarsa ta zuwa asibiti.

DUBA WANNAN: An garkame wani dalibin jami'a a jihar Kano a kan caccakar dan majalisa

"Sakamakon hakan, fusatattun matasa a unguwar suka garzaya zuwa gidan Simeon Abah wanda kawu ne ga wanda ake zargi da aikata kisar kuma suka banka wa gidan wuta wadda hakan ya yi sanadiyar konewar Salome Abuh 'yar shekaru 60. Wasu gidaje uku sun kone.

Tuni an tafi da gawar ta zuwa asibitin koyarwa da ke Anyigba domin binciken ainihin sanadin mutuwarta. Kazalika, rundunar 'yan sanda ta shirya wata tawaga ta musamman zuwa garin domin kare barkewar rikici yayin da ana cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel