Sokoto: An kori masu shara 550 saboda karbar albashi biyu da rashin zuwa aiki

Sokoto: An kori masu shara 550 saboda karbar albashi biyu da rashin zuwa aiki

Gwamnatin jihar Sokoto ta sallami ma'aikatan wucin gadi 550 masu sharar titi saboda karbar albashi sau biyu da kuma rashin zuwa wurin aiki.

A hirar wayar da tarho da ya yi da Daily Trust, Kwamishinan Muhalli na jihar, Sagir Bafarawa ya ce wasu daga cikin masu sharar su na karbar albashi daga hannun karamar hukuma da kuma gwamnatin jihar.

Ya kara da cewa an kuma kori wasu saboda ba su zuwa wurin aiki.

Bafarawa ya ce an dauki wannan matakin ne domin tsaftace aikin bayan an gano wannan barnar dake afkuwa.

DUBA WANNAN: An garkame wani dalibin jami'a a jihar Kano a kan caccakar dan majalisa

Ya ce, "Muna son mu mayar da jihar matsayinsa na baya na kasancewa daya daga cikin jihohi mafi tsafta a kasar nan."

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar tana gina manyan wurarren zubar da shara biyar a wurarre daban a jihar domin inganta tsaftacce muhalli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel