Dalilai 7 da suka janyo wa PDP shan kaye a hannun APC a Bayelsa

Dalilai 7 da suka janyo wa PDP shan kaye a hannun APC a Bayelsa

A ranar Lahadi, 17 ga watan Nuwamba ne Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar da cewa dan takarar jam'iyyar APC, David Lyon shine wanda ya yi nasarar lashe zaben gwamna na jihar Bayelsa.

Tun a shekarar 1999 da Najeriya ta dawo mulki Demokradiyya, jam'iyyar PDP ce ta rika mulki a jihar Bayelsa amma jam'iyyar APC ta kawo karshen hakan da nasarar da tayi a zaben na Nuwamban 2019.

Legit.ng ta yi fashin baki kan wasu dalilai da suka haifar wa PDP shan kaye a jihar mai arzikin man fetur.

1. Tsayar da dan takara mara farin jini

Tun daga lokacin da ya yi nasara a zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a jihar, al'umma da dama ba su kaunar Duoye Diri. An gano cewa mutanen jihar sun fi son Timi Alaibe da Diri ya kayar.

Tsohon kakakin APC da ya fice a jam'iyyar ya yi hasashen cewa PDP za ta fadi zabe a jihar inda ya ce dan takarar da PDP ta tsayar bai kai na APC farin jini ba.

2. Rikicin cikin gida na jam'iyyar PDP

Akwai matsaloli da yawa dake faruwa a jam'iyyar ta PDP a jihar da ya yi dalilin shan kayen PDP a babban zaben 2015 inda Buhari ya lallasa Jonathan a zabe.

Rikicin na jam'iyyar ne ya yi sanadiyar tsige kakakin majalisar jihar a baya-bayan nan.

3. Sauya sheka

Sakamakon rashin warware matsalolin dake jam'iyyar, wasu daga cikin 'yan'yan jam'iyyar sun ta ficewa suna komawa APC gabanin zaben.

Babu shakka hakan ya sake karya gwiwar jam'iyyar a jihar da karfafa APC.

4. Salon mulkin Gwamna Serike Dickson

Jim kadan kafin zaben, Sanata Nimi Amange, tsohon sanata mai wakiltan mazabar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a jam'iyyar PDP ya yi hasashen cewa APC za ta yi nasara.

Amange ya ce ya fice daga PDP ne saboda salon mulkin Gwamna Dickson da ya ce baya janyo mutane a jiki yayin da shima Robert Enoga yayin ficewa daga PDP ya ce kama karya da jam'iyyar ta sa ya fice.

5. Rashin samun kwakwaran goyon baya daga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Duk da cewa nuna a fili cewa baya goyon bayan dan takarar na PDP ba, wasu masu nazarin siyasa suna ganin Jonathan din bai nuna alamar cewa yana goyon Diri dari bisa dari ba.

Wata alama kuma itace yadda 'yan uwan Jonathan da dama suka koma APC daf da zabe kuma bai hana hakan ba.

Kamar yadda sakamakon INEC ya nuna, APC ta lallasa PDP a karamar hukumar Ogbia inda Jonathan ya fito.

DUBA WANNAN: An garkame wani dalibin jami'a a jihar Kano a kan caccakar dan majalisa

6. Samun goyon bayan Timpre Silver

A lokacin da dan takarar PDP bai samu goyon baya daga Jonathan ba, takwararsa na APC ya samu cikakken goyon bayan tsohon gwamnan jihar kuma karamin ministan man fetur a yanzu Timipre Silva. A Najeriya samon goyon bayan masu gidan siyasa abu ne mai muhimmanci.

7. Yawan al'umma

Dan takarar APC, Lyon ya fito ne daga karamar hukumar Ijaw ta Kudu wacce ta fi ko wanne karamar hukumar yawan kuri'u a jihar. A karamar hukumar APC ta samu kuri'u 124,803 yayin da PDP ta tashi da 4,898.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel