Matasa sun suburbudi gwamnan jiha yayinda ya fita kasar waje yawo (Bidiyo)

Matasa sun suburbudi gwamnan jiha yayinda ya fita kasar waje yawo (Bidiyo)

- Wani gwamnan jiha a kasar Congo ya ga rashin mutuncin mutanensa a kasar Faransa

- Gwamnan mai suna Gentiny Ngobila Mbaka ya ci mugun duka yayinda ya fita birnin Paris sayayya

- Matasa yan kasar Congo mazauna kasar Faransa ne suka yanke masa wannan hukunci

Matasan kasar Congo mazauna kasar Faransa sun ci mutuncin gwamnan jihar Kinshasha, Gentiny Ngobila Mbaka, wanda ya je yawon ganin ido kasar Faransa.

A bidiyon da ya bayyana a shafin ra'ayi da sada zumunta, an ga inda matasan ke jifansa da tutan kasar kuma suna watsa masa ruwa.

Wani matashi a shafin Tuwita, @uche_ezeonye wanda ya daura bidiyon ya ce dukkan yan siyasa musamman yan Najeriya ya kamata a rika yiwa irin wannan. Shin yarda da maganansa?

Kalli bidiyon:

A watan Agusta, irin wannan abun ya faru da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, yayinda ya kai ziyara kasar Jamus.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel