'Yan majalisa sun lalata tiriliyan daya da sunan aikin mazabu - Buhari

'Yan majalisa sun lalata tiriliyan daya da sunan aikin mazabu - Buhari

- Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce, kwalliya bata biya kudin sabulu ba a bangaren kudin da majalisa ta kashe

- Buhari ya ce, daga binciken da aka yi daga kauyuka da karkara, an tabbatar da cewa jama'a basu ci moriyar aiyukan ba

- Shugaban ya ce, an kashe tiriliyan daya a shekaru 10 da suka gabata don aiyukan habaka jama'a amma ba amo ba labari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce kwalliya bata biya kudin sabulu ba a bangaren kudin da majalisa ta kashe, wanda yawansa ya zarce tiriliyan daya, da sunan aiki a mazabu.

Buhari ya ce alkaluman da aka tattaro daga kauyuka da karkara sun tabbatar da cewa jama'ar da ke zaune a wadannan wurare basu ci moriyar wani aiki ba duk da an karbi kudi da sunan yi musu aiyuka.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wurin wani taro da aka shirya domin nuna kyama ga cin hanci a tsakanin ma'aikata da jagororin al'umma.

DUBA WANNAN: Zaben Kogi: IGP ya bayyana dalilin yin amfani da jirgi mai saukar ungula domin jefo barkonon tsohuwa

Shugaba Buhari ne ya bude taron wanda ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya shirya a fadar gwamnati da ke Abuja.

Taron ya samu hadin gwuiwa da hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da laifuka masu nasaba da almundahana.

"An kashe tiriliyan daya da sunan aiki a mazabu a cikin shekaru 10 da suka wuce, amma zai yi wuya kaga inda aka kashe kudi," in ji Buhari.

Shugaba Buhari ya bukaci hukumar ICPC ta shiga farautar 'yan kwangilar da suka karbi kudi domin yin irin wadannan aiyuka da kuma abokan harkallarsu a cikin gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel