EFCC ta gano fursunan da ya yi damfarar $1m daga gidan yarin da yake tsare

EFCC ta gano fursunan da ya yi damfarar $1m daga gidan yarin da yake tsare

Bullowar bayanin abun kunyar da ya faru, ta yadda wani dan gidan yari da ke zaman hukuncin shekaru 24 a kan laifin damfara ya cigaba da tattara kazamar dukiya a gidan ya girgiza mutane. Hakazalika, hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta bazama don bankado irin aika-aikar da ke aukuwa tsakanin manyan 'yan sanda tare da manyan jami'an gidajen kurkukun Najeriya.

Rahotannin da hukumar EFCC ta samu sune, wani dan damfarar yanar gizo, Hope Olusegun Aroke, wanda a halin yanzu yake gidan mazan inda zai yi shekaru 24 a gidan yarin Kirikiri da ke Legas, ya yi nasarar hada kai da jami'an 'yan sanda tare da hukumomin gidan yarin inda ya kara damfarar dala miliyan daya.

Abun ban mamakin shine, yadda mutumin da aka tura gidan don tsareshi na shekaru 24, yake fita asibitin 'yan sanda na jihar Legas tare da yawon otal-otal da sauran wuraren shakatawa don aiwatar da miyagun aiyukansa.

DUBA WANNAN: APC: Na ji ciwon cin amanar da Shuaibu ya yi min - Oshiomhole ya koka

Kamar yadda mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da wannan cigaban ga jaridar Vanguard a ranar Talata. Binciken farko ya nuna cewa, dan gidan yarin na amfani da yanar gizo tare da wayarsa a gidan gyaran halin na Kirikiri inda yakamata a ce yana daure ne.

"Abun mamakin shine, yadda Aroke ya sa aka kwantar dashi a asibitin 'yan sanda, Falomo, jihar Legas a kan ciwon da ba a bayyana ba. Daga asibitin yake zuwa dakin otal ya hadu da matarsa da 'ya'yansa biyu har kuma su halarci wuraren shakatawa," Uwujaren ya ce.

"Dalilin kwantar da shi da kuma wadanda suka taimaka masa ya fita daga asibitin zuwa otal din da sauran wajen shakatawar ne ake bincike har yanzu,

"Bincike ya nuna cewa, Aroke ya yi amfani da wani suna don bude asusun banki har biyu. Ya siya kadara a Lekki har ta naira miliyan 22 da kuma mota kirar Lexus wacce ya siya da sunan matarsa.

"Cigaba da bincike ya nuna cewa, wanda ake zargin ya siya wani gidan bene mai dakunan barci hudu a Lekki na naira miliyan 48, yayin da ake shari'arsa a 2015." in ji mai magana da yawun EFCC din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel