Jama'a sun banka wa wani mutum da ake zargi da satar babur

Jama'a sun banka wa wani mutum da ake zargi da satar babur

Wani mutum da ake zargi da satar babur wanda har yanzu ba a san sunansa ba ya ci wuta inda ya kone kurmus. Fusatattun jama'ar kauyen Dafa na karamar hukumar Kwali da ke Abuja ne suka babbaka shi.

Wani ganau ba jiyau ba mai suna Musa Isma'ila, ya ce lamarin ya faru ne wajen karfe 7:30 na safiyar yau lokacin da mamacin ya saci babur daga ma'ajiyarsa da ke bayan wani gida a kauyen.

Ya ce, mai babur din ya aje shi ne ta bayan wani gida inda ya shiga gidan don ganin makwabcinsa. Tuni barawon babur din ya saka wani mabudi ya bude tare da tserewa da babur din.

DUBA WANNAN: Yadda 'yan sanda suka kashe mutum 2 yayin tukin ganganci

Ya kara da cewa, lokacin da mai babur din ya gano cewa an sace masa abun hawan nasa, sai yayi kururuwa tare da neman dauki daga jama'a. Masu baburan haya basu yi kasa a guiwa ba suka bazama inda suka cafke wanda ake zargin yana dab da shiga Kwali.

"Bayan sun samu nasarar tsare wanda ake zargin barawon babur din ne, ya ciro wukake inda ya hari mutane biyun farko da suka yi yunkurin cafkesa. A rashin sa'arsa, sauran mutanen da ke biye dashi sai suka bayyana tare da fin karfinsa inda suka halakashi a take," in ji shi.

Duk wani yunkurin jin ta bakin mukaddashin mai magana da yawun hukumar 'yan sandan birnin tarayyar, ASP Maryam Yusuf, ya tashi a tutar babu saboda bata dau kiraye-kirayen wayarta da aka dinga ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel