Daukaka kara: Kotu ta yi watsi da bukatar APC na neman a soke kujerar Gwamna Ihedioha

Daukaka kara: Kotu ta yi watsi da bukatar APC na neman a soke kujerar Gwamna Ihedioha

Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Emeka Ihedioha a matsayin gwamnan jihar Imo. Jastis Oyebisi Omoleye ce ta jagoranci kungiyar alkalan biyar da suka zartar da hukuncin a ranar Talata. Jam'iyyun APGA da APC ne suka daukaka karar da ke kalubalantar nasarar gwamnan.

Masu daukaka karar sun ce gwamnan bai samu daya bisa hudu ba cikin a kalla biyu bisa ukun kananan hukumomin jihar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanadar.

A don haka ne masu daukaka karar suka bukaci kotun da ta jingine hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe tare da maye gurbinsa da wani dan takarar ko ta sa a canza zabe a jihar.

Kotun ta fara sauraron daukaka karar ne daga Mista Uche Nwosu na jam'iyyar APGA amma daga baya ta rike sukar farko ta jam'iyyar PDP da gwamna Ihedioha suka yi.

DUBA WANNAN: Yadda 'yan sanda suka kashe mutum 2 yayin tukin ganganci

Kamar yadda kotun ta sanar, tun farko yakamata ta yi watsi da daukaka karar amma biyayya ga umarnin kotun koli ta sa suka cigaba da saurarar daukaka karar.

Bayan sauraro tare da nazarin koken Nwosu da jam'iyyar APGA, Jastis Omoyele ta bukaci tarar N500,000 daga garesu.

Kotun ta kara da yin watsi da daukaka karar da Sanata Hope Uzodinma da APC suka yi saboda rashin madogara. An ci su tarar N500,000.

Hakazalika, daya daga cikin alkalan ya soki daukaka karar da Gwamna Ihedioha yayi tare da umartarsa da biyan tarar naira miliyan daya ga sanata Uzodinma da jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel