An garkame wani dalibin jami'a a jihar Kano a kan caccakar dan majalisa

An garkame wani dalibin jami'a a jihar Kano a kan caccakar dan majalisa

Yahuza Tijjani, dalibin jami'ar Bayero da ke Kano na garkame a gidan gyaran hali bayan da aka gurfanar dashi a gaban wata kotun majistare.

An gurfanar da Yahuza Tijjani ne a gaban kotun sakamakon kalubalantar dan majalisa Kabiru Isma'il da ya yi.

Dalibin shekara ta biyu a bangaren karatun kimiyya da fasaha ta jami'ar Bayeron ya kalubalanci dan majalisar ne a kafar sada zumunta ta Facebook. An ruwaito cewa, dalibin bai ambaci sunan dan majalisar ba a rubutun nasa na kalubale da ya wallafa a Facebook din.

'Yan sanda sun cafke Yahuza Tijjani ne tun a ranar 30 ga watan Satumba a karamar hukumar Madobi da ke jihar Kano, Murtala Tijjani, dan uwan dalibin ya sanar da jaridar Premium Times.

Tijjani yace, kaninsa ya yi kwanaki 7 a hannun 'yan sandan kafin kotun majistare ta iza keyarsa zuwa gidan maza.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Hadimin Atiku na kut-da-kut ya rasu

Dan majalisar da Tijjani duk 'yan asalin karamar hukumar Madobi ne a jihar Kano. Wata kungiyar magoya bayan dan majalisar sun caccaki dalibin tun farko a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook.

Dan uwan Tijjani ya ce, "Yanzu abun damuwarmu shine, akwai yuwuwar korarsa daga jami'a saboda bai rubuta jarabawar duka zangon karatun nan da ya gabata ba. Akwai yuwuwa ya cigaba da zama a gidan mazan tunda duk wata hanya da zamu bi don a sako shi mun bi kuma hakan ya gagara."

Dan uwansa yace, alkalin kotun ya bada belinsa tun lokacin zaman kotun amma karkashin tsauraran sharudda wadanda suka kasa cikawa.

Daga bisani kuwa, alkalin ya ce fayel din shari'ar ya bar ofishinsa an mika ma'aikatar shari'a. 'Yan uwansa sun garzaya amma an hanasu ganin shugaban alkalan jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel