Babu ma'aikacin da ke bi na sisin kwabo - Gwamna Yahaya Bello

Babu ma'aikacin da ke bi na sisin kwabo - Gwamna Yahaya Bello

Bayan hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar da sakamakon zaben gwamna na jihar Kogi a ranar Litinin inda ta bayyana cewa dan takarar jam'iyyar APC, Yahaya Bello ne ya lashe zaben na ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba. Zababben gwamnan, Yahaya Bello, a ranar Talata yayin zantawa da manema labarai ya musanta ikirarin cewa ma'aikata na bin bashin albashi a jihar inda ya ce duk karya ne.

A cewar rahotannin, Bello ya jadada cewa baby wani ma'aikaci da ke bin gwamatinsa bashin albashi domin tuni ya biya dukkan ma'aikatan jihar basusukan da suke bi.

Lailanews ta ruwaito cewa zababen gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin zantawa da ya yi da Channels Television inda ya kara da cewa 'yan daba na jam'iyyar PDP ne suka daba wa wani magidanci wuka bayan an sanar da cewa shi ne ya yi nasara a zaben na ranar Asabar.

Ya ce, "Dukkan rahotanin da ake yadawa na cewa bana biyan albashi karya ne. Tsaffin gwamnoni da suka gabace ni duk ana bin su bashi tun daga Audu har zuwa wanda na gada. Ba a bin jihar Kogi bashin albashi a halin yanzu, abinda da ya rage kashi 10 ne cikin 100 na basusukan da ake bin gwamnatocin baya.

DUBA WANNAN: Daga karshe: Buhari ya warware sarkakiyar sallamar hadiman Osinbajo 35

"Batun durkusawa da El-Rufai ya yi, ya yi hakan ne don rokon mutanen Kogi su yafewa Bello saboda ya samar da tsaro ba wai domin ya kasa biyan albashi ba.

"Bayan an sanar da cewa ni na lashe zabe, wani dan daba na PDP ya dabawa wani wuka ya tsere cikin gidan mata amma an kamo shi kuma an dauki mataki a kansa.

"An harbi matar mataimakina amma cikin ikon Allah ba ta mutu ba, 'yan sanda suna bincike a kan lamarin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel