APC: Na ji ciwon cin amanar da Shuaibu ya yi min - Oshiomhole ya koka

APC: Na ji ciwon cin amanar da Shuaibu ya yi min - Oshiomhole ya koka

- Adams Oshimhole, shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya koka a kan zargin cin amanrsa da ya ce Philph Shaibu ya yi

- Shaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo, ya ce har yanzu Oshiomhole ubane a wurinsa a siyasa amma dai yanzu bashi da tasiri a siyasar jihar Edo

- Oshiomhole ya ce zai bi hanyar lalama wajen warware rigingimun da APC ke fama da su a jihar Edo

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya zargi mataimakin gwamnan jihar Edo, Philiph Shaibu, da cin amanarsa duk da irin halacci da ya yi masa wajen kai wa ga matakin da yake kai.

Duk da ya koka da irin cin amanar da ya ce Shaibu, wanda ya dauka tamkar da, ya yi masa, Oshiomhole ya ce zai bi hanyar lalama wajen warware rigingimun da APC ke fama da su a jihar Edo.

A nasa bangaren, Shuaibu ya musanta cewa ya ci amanar Oshiomhole tare da bayyana cewa shugaban jam'iyyar na APC bashi da wani tasiri yanzu a siyasar jihar Edo.

DUBA WANNAN: Buhari ya aika wa majalisar dattijai wasu sabbin kudiri guda 6

Amma, Oshiomhole ya bayyana mamakinsa a kan yadda Shaiabu da wasu 'yan siyasa daga karamar hukumarsa zasu juya masa baya, suke yakarsa, duk da irin gudunmawar da ya basu kafin su kai ga inda suke a yanzu.

Rikicin jam'iyyar APC a jihar Edo ya yi tsamari a makon jiya, lamarin da ya yi sanadin dakatar da Oshiomhole, gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, Shaibu, da sauransu daga tsagin shugabancin jam'iyyar APC daban-daban.

Da yake gabatar da jawabi yayin gana wa da wasu magoya bayan jam'iyyar APC da suka ziyarce shi a gidansa da ke mahaifarsa a jihar Edo, Oshiomhole ya bukaci jama'a su zauna lafiya tare da guje wa amfani da su wajen tayar da hankali saboda kudin kalikan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel