Zaben Kogi: IGP ya bayyana dalilin yin amfani da jirgi mai saukar ungula domin jefo barkonon tsohuwa

Zaben Kogi: IGP ya bayyana dalilin yin amfani da jirgi mai saukar ungula domin jefo barkonon tsohuwa

Babban sifeton rundunar 'yan sanda ta kasa (IGP), Mohammed Adamu, ya bayyana cewa jami'an 'yan sanda sun yi amfani da jirgin sama mai saukar ungulu wajen jefa barkonon tsohuwa domin hana barkewar rikici yayin zaben jihar Kogi da aka gudanar ranar Asabar.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan kammala taron shugabannin hukumomin tsaro da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Adamu ya bayyana cewa dole ce tasa jirgin saman da ke sintiri a sararin samaniya shiga rigimar da ta tashi a lokacin da wasu bata gari suka sace akwatunan zabe.

Ya kara da cewa rundunar 'yan sanda ta fito cikin shiri a ranar Asabar yayin zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi saboda bayanan da suka samu sun nuna cewa za a iya samun tashin hankali yayin zabe a jihohin biyu.

Tun kafin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da sakamako na karshe a zaben kujerar Sanatan jihar Kogi ta yamma, dan takarar jam'iyyar PDP, Sanata Dino Melaye, ya ce ba zasu amince da sakamakon zaben ba.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa jami'ar jihar Ekiti zata sallami ma'aikata 500

A wani faifan bidiyo da ya fitar, Melaye, ya bayyana cewar ba zabe aka yi a jihar Kogi ba.

"An yi amfani da sojoji, jiragen yaki da jami'an tsaro na gaske da na bogi domin firgita masu zabe. Amma duk da haka INEC ta cigaba da gudanar da zabe.

" An yi amfani da jami'an tsaro da bamu san na gaske ne ko na bogi ba wajen sace akwatunan zabe da kuma tafka magudin zaben.

"Muna da shaidu, mun saka hotuna a dandalin sada zumunta don kowa ya ga abinda ya faru, mune muka ci zabe amma sun murde mana. Ba zamu yarda ba, zamu bi hakkin mu," a cewar Dino Melaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel