Buhari ya aika wa majalisar dattijai wasu sabbin kudiri guda 6

Buhari ya aika wa majalisar dattijai wasu sabbin kudiri guda 6

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika wasu sabbin kudirai guda 6 zuwa majalisar dattijai

- Shugaban majalisar dattijai, Ahmed Lawan, shine ya karanta wasikar Buhari a zauren majalisar dattijai

- Dukkan sabbin kudiran 6 nada alaka da harkokin da suka shafi jirgin sama

A ranar Talata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika wasu kudiri 6, masu nasaba da harkar jiragen sama, zuwa majalisar dattijai domin mayar da su doka.

Sabbin kudiran 6 sune; ' Civil Aviation Bill, 2019; Federal Airports Authority of Nigeria Bill, 2019 and Nigerian College of Airspace Management Agency (Establishment) Bill, 2019;

Sauran sun hada da 'Nigerian College of Aviation Technology (Establishment) Bill, 2019; Nigerian Meteorological Agency (Establishment) Bill, 2019 and Nigerian Safety Investigation Bureau (Establishment) Bill, 2019.

DUBA WANNAN: Buhari ya aika sako ga wadanda sakamakon zaben Bayelsa bai yi wa dadi ba

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban kasa ya aika wa shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, kuma aka karanta ta a zauren majalisar dattijai.

A cikin wasikar, shugaba Buhari ya bayyana cewa ya aika wa majalisar wasikar ne domin yin biyayya ga sashe na 58 na kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 1999.

Bayan ya kammala karanta wasikar, Lawan ya umarci magatakardan majalisa da ya tattara bayanai a kan kudiran tare da buga kwafin da zai raba wa mambobin majalisar domin su yi duba na tsanaki kafin a fara mahawara a kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel