Yanzu Yanzu: Gbajabiamila ya rantsar da sabbin mambobin majalisar wakilai 3

Yanzu Yanzu: Gbajabiamila ya rantsar da sabbin mambobin majalisar wakilai 3

- Mista Femi Gbajabiamila, akakin majalisar wakilai ya rantsar da sabbin yan majalisar wakilai guda uku

- Wadannan sabbin yan majalisa za su maye gurbin wasu korarrun yan majalisa da kotuna daban-daban suka tsige su

- Sabbi mambobin majalisar sune; Samson Okwu (jihar Benue), Obinna Chidoka (jihar Anambra) da kuma Chinedu Ogah (jihar Ebonyi)

Kakakin majalisar wakilai, Mista Femi Gbajabiamila, ya rantsar da sabbin yan majalisar wakilai guda uku.

Wadannan sabbin yan majalisa za su maye gurbin wasu korarrun yan majalisa da kotuna daban-daban suka tsige su.

Gbajabiamila ne ya jagoranci rantsuwar kama aiki da sabbin yan majalisar suka dauka a zauren majalisa a yau Talata, 19 ga watan Nuwamba.

Magatakardar majalisar, Patrick Giwa ne ya shirya taron rantsarwar ya Samson Okwu (jihar Benue), Obinna Chidoka (jihar Anambra) da kuma Chinedu Ogah (jihar Ebonyi).

KU KARANTA KUMA: Zaben Kogi: Dino Melaye ya yi barazanar kai karar Gwamna Yahaya Bello gaban ICC

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Majalisar dattawa a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba, ta rantsar da Sanata Abdullahi Danbaba mai wakiltan Sokoto ta Kudu.

Danbaba na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya maye gurbin Shehu Tambuwal (daga All Progressives Congress) wanda kotu ta sallama a kwanan nan.

Dan majalisar na PDP ya kuma dauki rantsuwar kama aiki a lokacin bikin rantsarwar.

Ku tuna jam’iyyar Legit.ng ta rahoto cewa a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba, kotun daukaka kara ta tsige Tambuwal, mai wakiltan Sokoto ta kudu a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel