Dalilin da yasa jami'ar jihar Ekiti zata sallami ma'aikata 500

Dalilin da yasa jami'ar jihar Ekiti zata sallami ma'aikata 500

Tashin hankula da tunanin kan wa abun zai fada ya yawaita ga ma'aikatan jami'ar jihar Ekiti (EKSU) Ado-Ekiti. An zargi wani yunkurin hukumar jami'ar na sallamar ma'aikatanta 500, jaridar TribuneOnline ta gano.

Kamar yadda majiyar ta ce, wadanda abin ya shafa sune ma'aikatan da aka dauka zamanin shugabancin farfesa Samuel Oye Bandele a jami'ar.

Daya ga cikin ma'aikatan da abun ya shafa, ya zanta da jaridar TribuneOnline amma da bukatar a boye sunansa. Ya ce, sabon shugaban kwamitin zartarwar jami'ar kuma babban shugaban jami'ar, Farfesa Bamitole Omole ya nuna damuwarsa a kan abinda ya kwatanta da yawa ba na misali ba na ma'aikata a jami'ar.

Majiyar ta ce: "Eh, da gaske ne, hukumar makarantar nan ba da jimawa ba zata bada takardun sallama saboda koken cewa ma'aikatan jami'ar sun yi yawa.

DUBA WANNAN: Buhari ya aika sako ga wadanda sakamakon zaben Bayelsa bai yi wa dadi ba

"An sanar damu cewa, ko yaushe za a iya fara bada wasikar sallamar. Hakan yasa kowa ke cikin tsoro da tashin hankula."

An kara gano cewa, farfesoshi da aka karawa girma ba ta yadda ya dace ba za a rage musu girma.

Kungiyar malamai masu koyarwa ta jami'ar(ASUU) a watan Satumba ta yi barazanar tafiya yajin aiki sakamakon rashin biyan albashi da jami'ar ta ke yi.

Shugaban ASUU na jami'ar, Dr Kayode Arogunde, ya bayyana cewa jimillar albashin ma'aikatan jami'ar na wata daya ya yi tashin gwauron zabi daga N380 million zuwa N502 million. Kuma gwamnati a wata daya tana ba jami'ar N260 million inda ta ke barin jami'ar ta samo N262million da kanta.

Jami'in hulda da jama'ar jami'ar, Bode Olofinmuagun, ya musanta wannan shirin.

"Babu wata damuwa da tashin hankula da jami'ar ke fama da ita a kan sallamar ma'aikata. Ina cikin makaranta a halin yanzu da nake magana da kai. Lafiya kalau kuwa ake don babu wannan shirin," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel