Abba Vs Ganduje: Yadda ta kaya a zama na farko a kotun daukaka kara

Abba Vs Ganduje: Yadda ta kaya a zama na farko a kotun daukaka kara

- Kotun daukaka kara ta gudanar da zama na farko a karar da PDP da dan takararta na gwamna a jihar Kano suka daukaka

- Ranar 2 ga watan Oktoba ne kotun sauraron korafin zaben gwamnan jihar Kano ta tabbatar wa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje nasarar da ya samu

- PDP da Abba sun garzaya kotun daukaka karar ne saboda basu gamsu da hukuncin da kotun sauraron korafin zabe ta farko ba ta zartar

Kotun daukaka kara da ke zamanta a jihar Kaduna ta ce zata yanke hukunci a kan karar da da jam'iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, suka daukaka.

A ranar 2 ga watan Oktoba ne kotun sauraron korafin zaben gwamnan jihar Kano ta tabbatar wa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje nasarar da ya samu.

Rashin gamsuwa da hukuncin da kotun farkon ta zartar shine yasa PDP da Abba suka daukaka kara.

DUBA WANNAN: Yadda a ka bi dare da duhu a ka kwacemin nasarar da na samu - Dino Melaye

Bayan kammala kammala sauraron kowanne bangare, kotun, mai alkalai biyar a karkashin jagorancin mai shari'a, Jastis Tijjani Abubakar, ta ce zata sanar da ranar da zata yanke hukunci ga wadanda abin ya shafa.

Jam'iyyar PDP da Abba sun samu wakilcin tawagar lauyoyinsu a karkashin jagorancin Adegboyega Awomolo (SAN), Barista Joseph Dawudu (SAN) shine wanda ya wakilci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), yayin da Offiong Offiong (SAN) da Barista Alex Iziyon (SAN) suka wakilci jam'iyyar APC.

Ragowar alkalan kotun sun hada da Jastis Paul O. Elechi, Muhammad Mustapha, G. O. Kolawole da Abubakar Umar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel