Zaben Kogi: Mutane 10 sun mutu, wurare 79 akayi rikici - CDD

Zaben Kogi: Mutane 10 sun mutu, wurare 79 akayi rikici - CDD

Cibiyar raya demokradiyya, CDD, a ranar Litinin, ta bayyana cewa akalla mutane 10 suka rasa rayukansu a wurare 79 da akayi rikicin zabe a jihar Kogi ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2019.

Cibiyar ta bayyana cewa rikice-rikicen ya hada da kwace kayayyakin zabe daga hannun jami'an INEC da wasu yan baranda sukeyi, garkuwa da ma'aikatan INEC, sayen kuri'u, hare-hare kan masu lura da zabe, da barazana ga jama'a.

Hakazalika kada kuri'an kananan yara, sace akwatunan zabe, kada kuri'a fiye da sau daya.

A lissafi cikin kashi 100, rikice-rikeci ya kwashe kashi 66.21%, sayen kuri'a na da kashi 28.88% sannan kada kuri'an kananan yara kashi 5.41%.

Kananan hukumomin da rikici ya faru sune Lokoja, Kabba-Bunu, Ijumu, Okene, Ajaokuta, Dekina da Olamaboro saboda su suka fi yawan jama'a.

DUBA NAN Malamai sun gani a mafarki cewa zan zama shugaban kasa - Sani Yariman Bakura

Mun kawo muku rahoton cewa Hukumar gudanar da zabe ta kasa wato INEC ta alanta da Alhaji Yahaya Bello na jam'iyyar All Progressives Congress APC matsayin zakaran zaben gwamnan da aka gudanar ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2019.

Yahaya Bello ya lashe kuri'un kananan hukumomi 12 yayinda babban abokin hamayyarsa na PDP, Musa Wada, ya kashe kananan 11.

Baturen zabe ya bayyana cewa Yahaya Bello ya samu jimillar kuri'u 406,222 yayinda Musa Wada na PDP ya samu kuri'u 189,704.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel