Zaben Kogi: Dino Melaye ya yi barazanar kai karar Gwamna Yahaya Bello gaban ICC

Zaben Kogi: Dino Melaye ya yi barazanar kai karar Gwamna Yahaya Bello gaban ICC

Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa zai kai karar Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da wasu mutane da dama a gaban kasashen duniya sannan ya kuma kai su gaban kotun ICC kan rikicin da ya afku a lokacin zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamba.

Melaye ya rasa dan uwansa a rikicin bayan yan bindiga sun bude wuta a mazabarsa ta Aiyetoro.

Dan majalisan ya bayyana a wani rubutu da ya wallafa a shafin Twitter cewa zai kai lamarin gaban kasashen duniya, cewa abunda aka yi a Kogi ba zabe bane illa yakin basasa.

“Abunda ya gudana a Kogi ba zabe bane, abunda muka fuskanta yakin basasa ne da ya yi sanadiyar rasa ran mutane 16 zuwa yanzu. Zan yi karar Bello Smart Adeyemi, Taofik, Speaker Kolawole da Sunday Faleke zuwa gaban kasashen duniya sannan na karasa zuwa gaba. Wannan alkawari ne,” ya rubuta.

A ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar da Bello a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 16 ga watan Nuwamba sannan ta kaddamar da wanda aka sake na Kogi ta Kudu a matsayin ba kamalalle ba.

KU KARANTA KUMA: Zaben Bayelsa: Yar’Adua ya taya David Lyon murna

A halin da ake ciki, mun ji cewa wasu da ake zargin 'yan bangar siyasa ne sun kone wata mata a gidanta da ke Ochadamu, karamar hukumar Ofu da ke jihar Kogi kurmus.

Abun ya faru ne bayan zaben da aka yi na kujerar gwamnan jihar da aka yi a ranar Asabar da ta gabata. Matar mai suna Acheju Abuh itace shugaban mata ta jam'iyyar PDP a gundumar Wada/Aro na yankin.

An kurmusheta ne kuwa a ranar Litinin da rana bayan da 'yan dabar suka zarge ta da biyayya ga jam'iyya mai mulki.

A gano cewa, 'yan daban sun kusta cikin gidan matar ne da wajen karfe 2 na rana inda suka rufe duk wata hanya da zata iya fita. Sun watsa fetur a gidan tare da kunna wuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel