Zaben Bayelsa: Yar’Adua ya taya David Lyon murna

Zaben Bayelsa: Yar’Adua ya taya David Lyon murna

- Abdul-Aziz, kanin marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'Adua, ya taya David Lyon na jam'iyyar APC a Bayelsa murna kan nasarar da ya yi a zabe

- Yar'Adua ya bukaci Lyon da ya yi iya bakin kokarinsa domin mutanen jihar su ci moriyar damokradiyya

- Kanin marigayin shugaban kasar ya kuma mika godiya ga magoya bayan APC kan kokarinsu da ya yi sanadiyar nasarar jam'iyyar a jihar

Bayan kaddamar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Bayelsa, dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), David Lyon, na ta samun sakonnin taya murna daga magoya bayansa da makusantansa, musamman a fanin siyasa.

Daya daga cikin wadanda suka taya Lyon murna a baya-bayan nan shine Abdul'Aziz Musa Yar'Adua, kanin marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'Adua.

Yar'Adua, wanda ya kasance jagoran kungiyar yan takarar jam'iyyar APC na kasa wato All Progressive Congress Aspirants Forum (APCAF), a sakonsa na taya murna ya yi kira ga Lyon a kan ya yi aiki sosai ga mutanen jiharsa domin su ci moriyar damokradiyya.

Bugu da kari, ya bukaci wadanda suka fadi zaben da su hada hannu tare da zababben gwamnan domin ba mazauna jihar da yan asalin cikinta abunda suka cancanta a rayuwa.

Kari kan haka, Yar'Adua ya jinjinawa Timipre Sylva, ministan man fetur, kan tattara mutanen Bayelsa da ya yi don ganin nasarar APC a jihar.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya aika sako ga wadanda sakamakon zaben Bayelsa bai yi wa dadi ba

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben da aka kammala kwanan nan a jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta kaddamar dashi a matsayin wanda ya lashe zabe.

INEC a ranar Lahadi ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar APC, Cif David Lyon, a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan ya samu kuri’u 352,552 wajen kayar da babban abokin adawarsa, Douye Diri na PDP wanda ya samu kuri’u 143,172.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel