Zaben Bayelsa: Douye Diri ya bukaci INEC da ta kaddamar dashi a matsayin wanda ya lashe zabe

Zaben Bayelsa: Douye Diri ya bukaci INEC da ta kaddamar dashi a matsayin wanda ya lashe zabe

- Douye Diri, dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben Bayelsa da aka kammala ya ce lallai shine ya lashe zaben

- Dan takarar ya yi ikirarin cewa sakamakon zabe daga dakin PDP ya nuna cewa shine ainahin wanda ya lashe zaben

- Diri ya yi ikirarin cewa ya samu jimlan kuri'u 98,502 wajen kayar da APC wacce ta samu 55,903, kafin a sauya gaba daya sakamakon zaben

Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben da aka kammala kwanan nan a jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta kaddamar dashi a matsayin wanda ya lashe zabe.

INEC a ranar Lahadi ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar APC, Cif David Lyon, a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan ya samu kuri’u 352,552 wajen kayar da babban abokin adawarsa, Douye Diri na PDP wanda ya samu kuri’u 143,172.

Diri, wanda ya jagoranci wasu yan takarar gwamna na sauran jam’yyun siyasa domin jawabi ga manema labarai a Yenagoa, a jiya Litinin, ya ce sakamakon zaben da aka samu daga bangaren PDP ya nuna cewa shine ainahin wanda ya lashe zaben sannan ya bukaci INEC da ta yi gaggawan kaddamar dashia matsayin wanda ya yi nasara.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Hadimin Atiku na kut-da-kut ya rasu

A cewarsa, sakamako daga bangaren PDP ya nuna cewa jam’iyyar ta samu kuri’u 98,502 wajen kayar da APC wacce ta samu kuri’u 55,903, kafin an sauya dukkanin sakamakon saboda APC.

A baya mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya dan takarar jam'iyyar APC, David Lyon murna a kan nasararsa a zaben 16 ga watan Nuwamba da aka yi a jihar Bayelsa.

Buhari, kamar yadda mai bada shawara gareshi na musamman a kan yada labarai ya sanar a sa'o'in farko na ranar Litinin, ya jinjinawa magoya bayan APC da 'yan Najeriya a jihar da suka sauke nauyinsu na 'yan kasa cikin lumana.

Ya nuna rashin jindadinsa a kan rashin rayukan da aka yi a Bayelsa sakamakon zaben. Ya kara da ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel