Yadda 'yan sanda suka kashe mutum 2 yayin tukin ganganci

Yadda 'yan sanda suka kashe mutum 2 yayin tukin ganganci

- Jami'an 'yan sanda sun murkushe wasu mutane biyu har lahira a yayin tukin ganganci

- Mazauna yankin da masu wucewa sun ce, jami'an 'yan sandan sun tsere bayan aikata barnar

- Ana zargin 'yan sandan ne da gudu a titi tare da hawa hannun da ba nasu ba yayin tukin

Mutane biyu ne 'yan sanda suka murkushe a sakamakon tukin ganganci da ake zarginsu da shi.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a kan karshen doguwar gadar da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Mutanen da jami'an 'yan sandan suka murkushe na kan babur ne duk da har yanzu ba a gano ko su waye ba.

Hadarin ya ritsa ne da farar mota kirar Toyota Hilux mai lambar mota GGE 960 DD tare da wani babur kirar Bajaj mai lamba MEK 418 VH.

Ganau ba jiyau ba sun ce, jami'an 'yan sandan sun tsere da gaggawa ba tare da taimakon wadanda suka murkushe din ba.

DUBA WANNAN: Yadda 'yan bindiga suka kashe mutum 18 a wani sabon hari a Zamfara

Masu wucewa tare da mazauna yankin sun fara taimakon wadanda abun ya ritsa dasu kafin isowar kungiyar masu taimakon gaggawa wajen.

Kwamandan yankin na hukumar kiyaye hadurra na jihar Ogun, Clement Oladele, ya ce mutane biyun daga cikin wadanda suka yi hatsarin sun rigamu gidan gaskiya.

Oladele ya ce, "Mutane uku ne suka yi hatsarin. Biyu daga cikinsu sun rasu inda daya ya samu raunika amma cibiyar taimakon gaggawa ta jihar Legas da ke Ojota ta kai musu dauki. Gawar wanda ya rasun tana ma'adanar gawarwaki a asibiti,"

"Wadanda ake zargi da haddasa hatsarin sun bi hannun da ba nasu ba inda suka yi karo da wadanda ke kan baburan," ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel