Yadda 'yan bindiga suka kashe mutum 18 a wani sabon hari a Zamfara

Yadda 'yan bindiga suka kashe mutum 18 a wani sabon hari a Zamfara

Tsagerancin 'yan bindiga ya dawo a jihar Zamfara bayan lafawar da ya yi sakamakon tattaunawar da gwamna Bello Matawalle da 'yan bindigar.

A sabon hari da suka kai da yammacin ranar Lahadi, sun halaka mutane 18 a Karaye, karamar hukumar Gummi ta jihar.

Mazauna yankin sun ce, wannan ne hari mafi muni da 'yan bindigar suka yi cikin watannin nan. Sunci karensu ba babbaka na sa'o'i da yawa amma babu kalubalen da suka fuskanta daga jami'an tsaro. Sun tabbatar da cewa, an samu mutane da yawa a mummunan lamarin ya ritsa dasu.

Mai bada shawara na musamman ga Gwamna Bello Matawalle a kan harkokin tsaro, Abubakar Dauran, ya tabbatar da harin tare da cewa, ramuwar gayya ce da ake zargin Fulani sun yi saboda kashe 'yan uwansu da aka yi a kasuwar gundumar Bardoki da ke Gummi a makonni biyu da suka gabata.

Dauran ya ce, rahoton da yake dashi na nuna cewa mutane 10 ne suka rasa rayukansu. Ya dora laifin harin a kan 'yan sa kai, wadanda ya ce sun kashe wasu Fulani a kasuwa.

DUBA WANNAN: Kasashe 25 na duniya masu karfin iko a 2019

Ya kara da cewa, 'yan sa kai bakwai aka kama a kan harin. Harin ya jawo mutuwar tsoffi da dama a lokacin.

"An soke aiyukan 'yan sa kan a jihar, amma har yanzu suna cigaba da aikinsu tare da lalata kokarin kawo zaman lumana da gwamnatin ke yi. Har yanzu ana kokarin tabbatar da zaman lafiyar."

Ya yi kira ga mazauna yankin da kada su tsorata da hare-haren, cewa gwamnatin ta ci karfin lamarin.

Mai magana da yawun rundunar sojin Operation Hadarin Daji, Oni Orisan, bai dauki kira da kuma sakon karta kwanan da aka aike masa ba.

A cikin shekarunnan, jihar Zamfara ta fuskanci hare-hare wanda ya yi sanadin rashin rayuka da dama a jihar. Cikin kankanin lokacin da Matawalle ya hau kujerarsa, ya samu yin sasanci da 'yan bindigar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel