VAT: Zainab Ahmed ta yi wa Majalisar Dattawa karin bayani

VAT: Zainab Ahmed ta yi wa Majalisar Dattawa karin bayani

Ministar kudi da kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki ta amsa tambayoyi da Majalisar tarayya a game da kara harajin kayan masarufi watau VAT da gwamnatin tarayya ta ke shirin yi.

A zaman da aka yi a majalisar dattawan kasar, Sanatoci sun bukaci Zainab Ahmed ta zayyano masu jerin kayan masarufin da aka cire su daga cikin wadanda sabon karin harajin zai shafa.

‘Yan majalisar tarayyar sun yi wani zama ne kafin a gayyaci jama’a domin jin fa’idar kara harajin VAT da gwamnati ta ke neman yi daga 5% zuwa 7.5% a kasafin kudin shekara mai zuwa.

Minista Zainab Ahmed ta sanar da kwamitim tattalin arzikin majalisar dattawan cewa karin da za ayi ba zai shafi ainihin kayan abinci, da kayan karatun boko da kuma kayan asibiti ba.

KU KARANTA: Buhari Yarbawa sun huro wuta a kan muzgunawa da Osinbajo

Bayan wannan zama ne majalisar dattawan kasar za ta gayyaci ‘Yan Najeriya domin su tofa albarkacin bakinsu a game da matakin da ake shirin dauka na kara VAT a fadin kasar.

Daily Trust ta rahoto cewa an yi wannan zama ne a Ranar Litinin 18 ga Watan Nuwamba. Kafin a iya kara VAT, dole sai majalisa ta yi wa dokar haraji na kasa wasu garambawul a Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta na neman sababbin dabarun samun kudin shiga ne domin ta iya aiwatar da kasafin kudin shekarar 2020. Najeriya ta na sa ran kashe fiye da Naira Tiriliyan 10 a badi.

Yanzu haka majalisar ta na kokarin ganin ta kammala aiki a kan kundin kasafin kudin 2020 da ke gabanta. Ana sa ran a gama komai har a mikawa shugaban kasa ya sa hannu a Watan nan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel