David Lyon ya kai wa Bola Tinubu ziyara har gidansa a Abuja

David Lyon ya kai wa Bola Tinubu ziyara har gidansa a Abuja

Mun samu labari cewa gwamnan da ke jiran gadon mulki a jihar Bayelsa, David Lyon, ya ziyarci daya daga cikin manyan Jagororin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu.

David Lyon wanda ya tsayawa jam’iyyar APC takarar gwamna a jihar Bayelsa a zaben da aka gama, ya kai wa Bola Tinubu ziyara ne a gidansa a Ranar Litinin, 18 ga Watan Nuwamban 2019.

Mista David Lyon ya gana da Jagoran jam’iyyar APC ne da yammacin Ranar Litinin a gidansa da ke Unguwar Asokoro a babban birnin tarayya Abuja, jim kadan bayan ya ziyarci fadar Aso Villa.

Hakan na zuwa ne bayan hukumar zabe na INEC mai zaman kanta, ta tabbatar da ‘dan takarar a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Bayelsa da aka gudanar Ranar 16 ga Watan Nuwamba.

KU KARANTA: Kogi: ‘Dan takarar PDP ya tafi Kotu ya ce Jami'an tsaro sun murde zabe

Gwamnan APC na goben ya na tare ne da Cif Timipre Sylva a lokacin da ya kai wa Bola Tinubu ziyara. Timipre Sylva, tsohon gwamna ne kuma daya daga cikin manyan kusoshin APC a jihar Bayelsa.

Yanzu haka Sylva, Minista ne a gwamnatin shugaba Buhari kuma ya taka rawar gani wajen karbe mulkin jihar Bayelsa daga hannun PDP. Wannan ne karon farko da jam’iyyar ta rasa jihar tun 1999.

Hadimin tsohon gwamnan na Legas ne ya bada labarin wannan ziyara. Mai daukar babban ‘dan siyasar kasar hoto ya wallafa hotunan zaman da aka yi a kan dandalin sada zumunta na Facebook.

Kafin nan idan ba ku manta ba, David Lyon tare da gwamnonin APC da shugaban jam’iyya na kasa sun kai irin wannan ziyara wajen shugaban kasa Buhari domin yi masa godiyar musamman.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel