An hukunta kusan duk wadanda su ka bar APC tare da Saraki – Shugaban APC

An hukunta kusan duk wadanda su ka bar APC tare da Saraki – Shugaban APC

A Ranar Litinin 18 ga Watan Nuwamban 2019, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya yi jawabi a kan Sanatocin da su ka tsere daga tafiyar APC tare da Bukola Saraki.

Adams Oshiomhole ya bayyana cewa mutanen Najeriya sun hukunta dukannin wadannan ‘yan majalisa da aka zaba a tutar APC amma su ka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a tsakiyar 2018.

Yayin da ya ke magana a fadar shugaban kasa inda ya jagoranci Jiga-jigan APC wajen gabatar da sabon gwamnan APC mai jiran-gado, Adams Oshiomhole ya ce Dino Melaye kadai ya rage yanzu.

Dino Melaye ya na cikin wadanda su ka sauya-sheka daga APC kafin zaben 2019, amma shi kadai ya iya rike kujerarsa. Daga baya kotu ta rusa nasarar Sanatan, aka bukaci a gudanar da wani zabe.

KU KARANTA: Sai bana aka yi zaben gaskiya a Bayelsa tun 1999 - Oshiomhole

“Ina tunanin Dino Melaye ne kadai ya ke ta fama yanzu, shi ma kamar yadda ku ke ganin zaben, Smart Adeyami ya ba sa ratar kuri’a fiye a 20, 000 duk da INEC ta ce zaben bai kammalu ba tukun.”

Shugaban jam’iyyar na kasa ya kara da cewa su na da yakinin cewa babu yadda za ayi Sanata Dino Melaye ya kamo tazarar kuri’u 20, 000 da ‘dan takarar APC ya ba shi a karashen zaben.

“Ina tunanin ya zama mana darasi mu sani cewa idan ‘yan siyasa su ka yi takara a wata jam’iyya, sai kuma su ka yi watsi da wannan jam’iyyar da ta kawo su, masu zabe su na nan za su jira su.”

Daga cikin sauran Sanatocin da su ka bar APC a Yulin 2018 akwai Rabi'u Kwankwaso, Suleiman Hunkuyi, Barnabas Gemade, Shaaba Lafiagi, Suleiman Nazif, Isa Misau, Usman Nafada, dsr.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel