Bayelsa: PDP ta na barazanar korar Tsohon Shugaban kasa Jonathan na wani lokaci

Bayelsa: PDP ta na barazanar korar Tsohon Shugaban kasa Jonathan na wani lokaci

Mun samu labari cewa babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta na tunanin daukar mataki mai tsauri a kan tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan a game da zaben jihar Bayelsa.

Kamar yadda mu ka samu labari a yau Litinin 19 ga Watan Nuwamban 2019, jam’iyyar adawar ta na fushi da yadda zaben jihar Bayelsa ya kaya da kuma rawar da Jonathan ya taka.

Ana zargin Goodlcuk Jonathan da yi wa jam’iyyar APC mai mulki aiki ta karkashin kasa a wajen zaben sabon gwamnan. Shi dai tsohon shugaban kasar ya karyata wannan rade-radi.

Majiyar ta ce PDP ta na iya dakatar da Jagoran na ta a kan kawancen da ya kulla da jam’iyyar APC wajen karbe jiharsa daga hannun PDP a karon farko tun da aka dawo mulkin farar hula.

Jim kadan bayan jam’iyyar APC ta samu nasara a zaben, aka hangi Jonathan da Mai dakinsa tare da wasu manyan kusoshin APC wanda gwamnan jihar Jigawa ya jagoranta a gidansa.

Tsohon shugaban kasar bai halarci babban gangamin da jam'iyyarsa ta shirya na karshe a Garin Yenagoa ba. Haka zalika an nemi gwamnan Ribas, Nyesom Wike, wurin taron an rasa.

Bayan cewa Jonathan bai marawa Douye Diri baya wajen zaben fitar da gwanin PDP ba, Mahaifiyar tsohon shugaban ta yi wa David Lyon addu'ar sa'a a lokacin da ya ziyarce ta.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban kasa Jonathan bai yi APC ba - Reno Omokri

Jam’iyyar PDP ta rasa jihar ne bayan ‘Dan takararta Sanata Douye Diri ya tashi da kuri’a 143, 172 yayin da Davd Lyon na jam’iyyar hamayya ya lashe zaben da kuri’u fiye da 352, 000.

Akwai radi-radin cewa Goodluck Jonathan ba ya tare da ‘Dan takarar da ake zargin gwamna Seriake Dickson ya kakabawa PDP. Amma ya nuna cewa za a hada-kai ayi aiki tare.

Tun kafin zaben Jonathan ya tabbatar da cewa babu abin da zai sa ya taimawa APC a jiharsa. Amma ganin yadda PDP ta sha kayi a jihar Neja-Deltan, aka fara zargin akwai hannunsa.

Wani daga cikin ‘Ya ‘yan jam’iyyar APC a Kudancin Najeriya ya bayyana cewa tun ranar da tsohon shugaban kasar ya gana da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa, APC ta ci zabe.

Kawo yanzu dai ba mu da cikakken rahoton matakin da jam’iyyar adawar ta ke shirin dauka. APC mai mulki a na ta bangaren, ta kira wani taron gaggawa na musamman a karshen mako.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel