Wada zai je kotun zabe, ya zargi INEC da ‘Yan Sanda da yi wa APC aiki

Wada zai je kotun zabe, ya zargi INEC da ‘Yan Sanda da yi wa APC aiki

‘Dan takarar jam’iyyar PDP mai adawa a zaben 16 ga Watan Nuwamban 2019, Wada Musa, ya kamanta zaben gwamnan da aka yi a Kogi kwanan nan a matsayin hambarar da kuri’un jama’a.

A wata hira da Manema labarai a Ranar Litinin, Injiniya Wada Musa ya misalta zaben gwamnan da juyin mulki, ya na mai aniyar zuwa gaban kotun korafin zabe domin a fito masa da hakkinsa.

Wada ya yi jawabi a gaban Manema labarai a garin Abuja inda ya nuna cewa bai yarda da sakamakon zaben ba. Dole in garzaya kotun karbar korafin zabe domin a karbo mani nasarata.

Injiniya Wada wanda ya rikewa PDP tuta a zaben ya ke cewa: “Abin da ya faru a Kogi yaki ne aka kitsawa damukaradiyya; an yi wa mutane juyin mulki, an yi karfa-karfa da karfin kan bindiga.”

“Kowa ya san cewa babu zaben da aka yi a Ranar 16 ga Watan Nuwamban 2019, abin da aka yi shi ne yakar mutane. ‘Yan sanda sun taimakawa ‘yan daban APC tafka magudi a wuraren zabe.”

KU KARANTA: Fayose ya tsoma baki a a zabukan Bayelsa da Kogi, ya ce an yi murdiya

‘Dan takarar hamayyar ya ke cewa wadannan ‘yan daba sun yi abin da su ka ga dama inda su ka rika harbe Bayin Allah, su na kashe su, su na tserewa da kayan zabe zuwa gidajen gwamnati.

An rubuta sakamakon da su ka ba APC nasara (aka mikawa hukumar zabe na INEC) ta sanar da abin da ya sabawa ra’ayin jama’a. Wada ya ce an yi amfani da jiragen ‘yan sanda wajen magudin.

“APC ta maida jihar mu filin dagar yaki. Akalla ba a kasara ba, an kashe Bayin Allah tara. An kuma raunata mutane da dama a yunkurin APC na cigaba da rike mulki ko ta wani irin hali.”

“Don haka abin bakin ciki ne ace INEC ta sanar da wannan sakamako da aka kaga duk da tulin abubuwan da su ka faru a abin da aka yi da sunan zaben.” A cewar Wada, don haka zai tafi kotu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel