Yanzu-yanzu: Bayan barazanar da aka yiwa Oshiomole, majalisar zantarwan APC za ta zanna ranar Juma'a

Yanzu-yanzu: Bayan barazanar da aka yiwa Oshiomole, majalisar zantarwan APC za ta zanna ranar Juma'a

Muddin ba'a samu wani canji ba, jam'iyyar All Progressives Congress, APC, za ta shirya zaman majalisar zantarwan jam'iyyar NEC ranar Juma'a, 22 ga watan Nuwamba, 2019.

Wannan ya biyo bayan barazanar da aka yiwa shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomole, cewa idan ba zaikira zaman majalisar ba, yayi murabus.

Majalisar zantarwan APC ta kwashe watanni 15 bata zauna ba.

Hakan ya faru duk da cewa kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC ya bukaci cewa an gudanar da zaman majalisar bayan watanni uku-uku, sau hudu a shekara.

Majiya mai karfi ya bayyanawa The Nation cewa da yammacin nan, an tura sakonni ga masu ruwa da tsaki na ganawa ranar Alhamis gabanin zaman majalisar ranar Juma'a.

Majalisar zantarwan jam'iyyar APC ta kunshi shugabannin jam'iyya da masu ruwa da tsaki a fadin tarayya gaba daya.

Wannan ya hada da shugaban kasa, mataimakinsa, shugaban majalisar dattawa, mataimakinsa, kakakin majalisar wakilai da mataimakinsa, dukkan gwamnonin jam'iyyar APC, da sauran su.

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel