Jami’ar Dutsinma ta nemi a saki Ma’aikacinta da ya ke tsare tun Agusta

Jami’ar Dutsinma ta nemi a saki Ma’aikacinta da ya ke tsare tun Agusta

Bayan kwanaki kimanin 109, jami’ar tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina ta fito ta ce shirun da aka ji game da Ma’aikacinta da aka dauke kwanaki ya fara zama abin tsoro da tada hankali.

Jami’ar ta yi magana ne a kan Abubakar Idris wanda wasu Miyagu su ka yi gaba da shi tun farkon Watan Agusta. Kawo yanzu babu wanda ya sake jin labarin halin da Malamin ya ke ciki.

Mukaddashin Darektan hulda da jama’a na jami’ar, Habibu Matazu, ya bayyana cewa Abubakar Idris, Malami ne a sashen harshe na jami’ar da aka fi sani da FUDMA da ke cikin jihar Katsina.

Jami’ar ta bakin Malam Matazu, ta bayyana awon gaba da Malam Abubakar Idris da aka yi a gidansa cikin tsakar dare a matsayin rashin sanin mutunci da kuma keta alfarmar ‘Dan Adam.

Matazu ya nuna cewa sace Abubakar Idris da aka yi ba tare da jin duriyarsa ba, ya tada hankalin mutanen jami’ar da kuma musamman danginsa. Ga jawabin da Darektan ya yi a madadin jami’ar.

KU KARANTA: CSO ta yi Allah-wadai da sace bacewar Abubakar Dadiyata

“Jim kadan bayan dauke Malamin, shugabannin jami’ar FUDMA sun yi zaman gaggawa na musamman inda su ka sanar da jami’an tsaron jihar Katsina lamarin bacewar Abubakar Idris.”

“Shugabannin jami’ar a na su shawarar sun sanar da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari wannan lamari inda ta nemi gwamnati ta kawo hanyar da za a kubuto da Malamin daga Miyagu.”

“Har yanzu babu wanda ya bukaci fansa a kansa. Jami’ar ta na shaidawa uwar kungiyar ASUU da reshenta na FUDMA cewa ba za ta huta ba har sai ta ga an ceto wannan Malami da aka sace.”

“A kokarin jajantawa Iyalin wannan Bawan Allah, Abubakar Idris, Jami’ar ta dauki matakin ba iyalin gudumuwa tare da kafa kwamitin mutane uku domin su je su ziyarci Iyalin na sa.”

A karshe Matazu ya ce su na kira ga wadanda su ka sace Malamin su taimaka su sake shi domin ya koma bakin aikinsa da kuma cikin Masiyansa. An kuma nemi jama’a su dage da addu’o’i.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel