Wa’iyyazu billahi: Ya kashe mahaifiyar da ta tsuguna ta haife shi da hannunsa

Wa’iyyazu billahi: Ya kashe mahaifiyar da ta tsuguna ta haife shi da hannunsa

Wata kotun Majistare na jihar Ebonyi, da ke zama a Abakaliki, a ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba ta tsare wani dan shekara 38, Ozibo Simon, a gidan maza kan zargin kashe mahaifiyarsa da ta haife sa, Misis Ozibo Felicia.

An tattaro cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba a garin Iziogo da ke karamar hukumar Izzi na jihar.

Wanda ake zargin, ya kashe mahaifiyarsa a ranar 14 ya watan Nuwamba, da wani adda da shebur lokacin da ta je gidansa domin ganinsa a gaban matarsa.

Da yake tona lamarin, wanda ake zargin Mista Ozibo Simon ya bayyana cewa mahaifiyarsa bata yi masa laifin komai ba, amma cewa a kullun yana yi mata kallon sanadiyar shigarsa kangi da wahalar rayuwa.

Ya Kara da cewa yana da dabi’ar shan wiwi, amma cewa a wannan ranar da lamarin ya afku, bai kasance cikin maye ba.

An gurfanar da mai laifin a ranar Litinin bisa tuhuma guda na aikata kisan kai.

Lauyan yan sanda, Barista Eze Ndubuako, ya fara ma kotu cewa laifin ya kara da sashi 319(1) na dokar ta’addanci Cap. 33, Vol. 1, na dokar jihar Ebonyi, 2009.

Mai shari’a na kotun, Nnenna Onuoha, baya bayar da belin mai laifin ba domin a cewarta, lamarin ya fi karfin kotun.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Kotun daukaka kara ta jaddada zaben Ishaku a matsayin gwamnan Taraba

Ta yi umurnin cewa a tsare mai laifin a cibiyar gyaran halayya na Najeriya, Abakaliki sannan cewa a tura lamarin zuwa ofishin DPP don jin shawararsu.

An dage shari’an zuwa ranar 6 ga watan Disamba, 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel