Daga samun nasara; sabon zababben gwamnan Bayelsa ya garzaya Aso Rock

Daga samun nasara; sabon zababben gwamnan Bayelsa ya garzaya Aso Rock

- Sabon zababben gwamnan jihar Bayelsa a zaben ranar Asabar da ta gabata ya garzaya fadar shugaban kasa

- Ya samu rakiyar gwamnan jihar Kebbi; Atiku Bagudu, gwamnan jihar Jigawa; Badaru Abubakar da karamin minstan man fetur

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun shiga ganawar sirri da Mista David Lyon, gwamnan da ya kafa tarihi a jihar Bayelsa

Sabon zababben gwamnan ya samu rakiyar gwamnan jihar Kebbi; Atiku Bagudu, gwamnan jihar Jigawa; Badaru Abubakar, da karamin ministan man fetur; Timipre Sylva.

An ga Mista Lyon tare da Sylva sun nufi ofishin shugaban ma'ikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, bayan isarsu fadar shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Tsara sakamakon zaben Bayelsa aka yi - YIAGA ta tona asiri

Sabon zababben gwamnan jihar Bayelsa, Mista David Lyon, ya ziyarci fadar shugaban kasa, Aso Rock, da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Ba a san dalilin ziyarar mista Lyon a fadar shugaban kasa ba saboda babu wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar a kan ziyarar.

Buhari da Lyon sun shiga ganawar sirri a daidai lokacin da aka wallafa wannan rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel