Nasarar APC: Dalilin da yasa muka ziyarci Jonathan har gida a Bayelsa - Ministan Buhari

Nasarar APC: Dalilin da yasa muka ziyarci Jonathan har gida a Bayelsa - Ministan Buhari

Shugabanni da manyan 'ya'yan jam'iyyar APC a jihar Bayelsa sun bayyana dalilin da yasa suka ziyarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, jim kadan bayan INEC ta sanar da cewa jam'iyyar APC ce ta lashe zaben kujerar gwamnan jihar.

Jagororin jam'iyyar APC sun ziyarci Jonathan ne a daidai lokacin da dumbin magoya bayan jam'iyyar ke can kan titunan jihar Bayelsa suna murnar nasarar da suka samu.

Daga cikin manyan 'ya'yan jam'iyyar APC da suka ziyarci Jonathan akwai Badaru Abubakar (gwamnan jihar Jigawa), Atiku Bagudu (gwamnan jihar Kebbi), Timipre Sylva (karamin ministan man fetur), Ita Enang (tsohon hadimin Buhari) da wasu da dama.

DUBA WANNAN: Tsara sakamakon zaben Bayelsa aka yi - YIAGA ta tona asiri

Da yake magana da manema labarai a kan dalilin ziyarar da suka kai wa Jonathan's, Timipre Sylva ya ce sun ziyarci tsohon shugaban kasar ne domin nema wa sabon zababben gwamnan jihar Bayelsa tubaraki.

"A matsayinsa na tsohon shugaban kasa, uba ne shi ga kowa, kuma bango da dole a jingina da shi matukar mutum yana bukatar ya tsaya daidai.

"A saboda haka ne muka kawo masa ziyara a matsayinsa na tsohon shugaban kasa kuma tsohon gwamnan jihar Bayelsa domin neman goyon bayansa da tubaraki a sabuwar gwamnatin da APC ta kafa.

"Mun zo ne domin gabatar masa da sabon zababben gwamnan jihar Bayelsa domin neman goyon bayansa a kokarin APC na sake gina jihar Bayelsa," a cewar Sylva.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel