Kaico! Wata mahaifiya ta kashe ‘ya’yanta mata guda 2 a jahar Imo

Kaico! Wata mahaifiya ta kashe ‘ya’yanta mata guda 2 a jahar Imo

Rundunar Yansandan jahar Imo ta sanar da kama wata mata mai suna Ukamaka Ezike wanda ake zarginta da kashe ‘ya’yanata mata guda biyu masu kananan shekaru, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mijin matar, kuma mahaifin yaran, mai suna Christian Ezike mazaunin unguwar Awo Idemili dake cikin karamar hukumar Orsu na jahar Imo ne ya kai kara ga Yansanda.

KU KARANTA: Murnar samun nasara: Jiga jigan gwamnonin APC sun ziyarci shugaba Jonathan a gidansa

A cewar mahaifin yaran, Christian, yace baya gari a ranar 15 ga watan Nuwamba, a wannan lokaci ne matarsa ta lakada ma yaransu uku dan banzan duka. Yaran sun hada da Kosarachukwu mai shekaru 4, Chinwendu mai shekaru 2 da Chinecherem yar wata biyu.

Christian ya shaida ma Yansanda cewa sakamakon dukan da yaran suka sha a hannun babarsu tasa aka garzaya dasu zuwa asibiti, inda a can Chinecherem da Chinwendu suka rigamu gidan gaskiya.

Kaakakin Yansandan jahar, SP Orlando Ikeokwu ya tabbatar da aukuwar lamarin, sa’annan yace tuni sun kaddamar da bincike domin gano musabbabin wannan danyen aiki da uwargida Ukamaka ta aikata.

“Mun fara gudanar da binciken kwakwaf domin bankado dalilin daya harzuka wannan mata ta tafka wannan ta’asa, saboda babu hankali a cikin wannan lamari.” Inji shi.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Legas ta sanar da kama Segun Mopoderun da laifin kashe makwabcinsa bayan kaurewar wata zazzafar musu a tsakaninsu, a jahar Legas.

Segun mazaunin layin Ogba-Aguda ne dake cikin unguwar Agege ta jahar Legas, ana zarginsa da laifin antaya ma makwabcinsa ruwan zafi mai suna Oposanwo Gbenga dan shekara 58, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Kaakakin Yansandan jahar, Bala Elkana ya bayyana cewa koda yake mamacin bai mutu a inda aka watsa masa ruwan zafin nan take ba, amma ya mutu ne a yayin da ak garzaya da shi zuwa wani babban asibiti.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel