Tsara sakamakon zaben Bayelsa aka yi - YIAGA ta tona asiri

Tsara sakamakon zaben Bayelsa aka yi - YIAGA ta tona asiri

YIAGA AFRICA, wata kungiyar matasa masu rajin tabbatar da adalci da dorewar dimokradiyya , ta ce alamu na nuni da cewa tsara sakamakon zaben jihar Bayelsa aka yi.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da cewa dan takarar jam'iyyar APC, David Lyon, shine wanda ya samu nasarar lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa da aka gudanar a ranar Asabar.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Farfesa Faraday Orunmuwese, baturen zaben gwamnan ya ce, Lyon ya samu jimillar kuri'u 352,552 yayin da babban abokin takararsa na jam'iyyar PDP, Duoye Diri, ya samu jimillar kuri'u 143,172.

Amma, a cikin wani jawabin da ta fitar ranar Litinin Litinin, YIAGA, ta ce akwai manyan alamomin tambaya a cikin sakamakon da INEC ta sanar.

Tun kafin a sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Kogi da Bayelsa, YIAGA ta bayyana cewa zata iya tantance cewar sakamakon da aka sanar ya yi daidai da zabin masu zabe ko akasin haka.

DUBA WANNAN: Abubuwa 6 da yakamata a sani game da gwamnan jihar Kogi da ya zarce

"INEC ta saki sakamakon zabe ba tare da ta gudanar da zabe a dukkan mazabun da ke jihar Bayelsa ba. INEC ta sanar da cewa APC ta samu kuri'u 352,552 ko kuma kaso 71% na kuri'un da aka kada, ita kuma PDP ta samu kuri'u 143,172 ko kaso 29% na kuri'un da aka kada.

" Wannan sakamakon bai yi daidai da alkaluman masu zabe (PVT) da suka zabi APC da PDP ba. Kamar yadda kididdigar YIAGA ta nuna bayan kiyasin da ta gudanar a kan PVT, APC za ta iya samun kaso 62% ko 46% na kuri'un da aka kada, ita kuma PDP zata iya samun kaso 52% ko 37%.

"Rashin samun hakan a sakamakon da INEC ta sanar ya nuna cewa an tsara sakamakon ne yayin da ake tattara shi," a cewar jawabin da YIAGA ta fitar.

YIAGA ta bayyana cewa tana amfani da dabaru na ilimi da fasahar zamani wajen fitar da kiyasin yadda sakamakon zabe zai kasance ta hanyar amfani da bayanan da wakilanta ke aiko mata daga cibiyoyin zabe.

Kungiyar ta dora alhakin magudin zaben da ake yi a Najeriya a kan INEC, jam'iyyun siyasa, jami'an tsaro da sauran wasu hukumomi da ke da hannu a aikin gudanar da zabe a wasu mazabu ko kuma 'kitsa' sakamakon zabe bayan jama'a sun kammala kada kuri'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel