Da dumi-dumi: Kotun daukaka kara ta jaddada zaben Ishaku a matsayin gwamnan Taraba

Da dumi-dumi: Kotun daukaka kara ta jaddada zaben Ishaku a matsayin gwamnan Taraba

- Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da zaben Darius Ishaku a matsayin gwamnan jihar Taraba

- Kotun ta kuma yi watsi da karar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta daukaka kan rashin inganci

- Ta yarda da kotun zaben cewa mai karar bata da dan takara a zaben gwamna na ranar 9 ga watan Maris 2019 a jihar Taraba

Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja a ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba, ta tabbatar da dawowar Darius Ishaku a matsayin gwamnan jihar Taraba.

Kotun, wacce ta riki tazarcensa a wani hukunci da ta zartar, ta kuma yi watsi da karar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta daukaka kan rashin inganci.

Kwamitin mutane biyar na kotun sun amince da hukuncin kotun zaben gwamnan jihar Taraba, wacce ta kori karar APC akan rashin sahihanci.

Kwamitin, a hukuncinsa, ya yarda da kotun zaben cewa mai karar bata da dan takara a zaben gwamna na ranar 9 ga watan Maris 2019 a jihar Taraba, sakamakon hana dan takararta Abubakar Danladi yin takara da Wata babbar kotun tarayya da ke Jalingo ta yi a ranar 6 ga watan Maris, 2019.

KU KARANTA KUMA: Zaben Kogi: Buhari ya taya Yahaya Bello murnar lashe zaben gwamna

A wani labari na daan, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya yi magana a game da zaben gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa da aka gudanar Ranar Asabar dinnan, 16 ga Watan Nuwamban 2019.

Mista Ayodele Fayose ya fito ya na mai cewa hukumar zabe na kasa mai zaman kanta watau INEC ta murde zaben.

Tsohon gwamnan bai yarda da ingancin zaben da aka shirya a jihohi biyun ba. A wani sako da tsohon gwamnan ya fitar ta dandalinsa na sada zumuntan zamani na Tuwita, ya zargi hukumar zabe na INEC da kuma jami’an tsaron Najeriya da tafka magudi a Kogi da Bayelsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel