Zaben Kogi: Buhari ya taya Yahaya Bello murnar lashe zaben gwamna

Zaben Kogi: Buhari ya taya Yahaya Bello murnar lashe zaben gwamna

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Yahaya Bello murnar lashe zaben gwamna a jihar Kogi

- Buhari ya kuma bayyana cewa Mista Yahaya Bello ya yi tsere mai kyau a zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamba, sannan kuma cewa ya yi nasara da kyau

- Ya mika ta'aziyya ga yan uwan wadanda suka rasa ransu a zaben

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamnan jihar Kogi, Mista Yahaya Bello ya yi tsere mai kyau a zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamba, sannan kuma cewa ya yi nasara da kyau.

Hakan na kunshe ne a wani sakon taya murna zuwa ga Bello, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar a matsayin wanda ya lashe zaben.

“Shugaban kasar ya bayyana zaben da nasarar dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin tsere da nasara mai kyau.

“Ya yaba na magoya bayan APC akan jajircewa da suka yi da tsayawa tsayin daka duk da lamari na rikici”, cewar wani jawabin fadar shigaban kasa daga hadiminsa, Mista Femi Adesina a ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba.

Ya kuma mika ta’aziyya ga yan uwan wadanda suka rasa ransu a lokacin zaben.

KU KARANTA KUMA: Zaben Bayelsa: Buhari ya taya zababben gwamnan Bayelsa David Lyon murna

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar gudanar da zabe ta kasa wato INEC ta alanta da Alhaji Yahaya Bello na jam'iyyar All Progressives Congress APC matsayin zakaran zaben gwamnan da aka gudanar ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2019.

Yahaya Bello ya lashe kuri'un kananan hukumomi 12 yayinda babban abokin hamayyarsa na PDP, Musa Wada, ya kashe kananan 11.

Baturen zaben jihar Kogi, wanda ya kasance shugaban jam'iyyar Ahmadu Bello ABU Zariya, Farfesa Ibrahim Umar, ya sanar da hakan Lokoja, babbar birnin jihar Kogi Ya bayyana cewa Yahaya Bello ya samu jimillar kuri'u 406,222 yayinda Musa Wada na PDP ya samu kuri'u 189,704.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel