Yanzu Yanzu: Mutane 5 sun mutu yayinda tankar mai ta kama da wuta a Kogi

Yanzu Yanzu: Mutane 5 sun mutu yayinda tankar mai ta kama da wuta a Kogi

- Mutane biyar sun hallaka yayinda wata tankar mai ta kama da wuta a kewayen yankin Felele, hanyar babban titin Abuja-Lokoja

- Lamarin ya afku ne sanadiyar barkewar da birki ya yiwa motar, inda ta turmushe wasu motoci biyar a babban gidan man NNPC a Felele

- Matasa a yankin sun gudanar da zanga-zanga sanadiyar faruwar lamarin

Akalla mutane biyar ne suka hallaka a wani hatsarin tanka da ya afku a kewayen yankin Felele, hanyar babban titin Abuja-Lokoja.

Wata tankar mai cike da fetur wacce ta fito daga Lagas, ta samu ballewar birki, inda ta turmushe wasu motoci biyar a babban gidan man NNPC a Felele, Lokoja, jihar Kogi.

Lamarin ya yi sanadiyar barkewa zanga-zanga a tsakanin matasa da ke yankin.

A wani labari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, a ranar Juma'a ya zubar da hawaye yayinda yaga wadanda suka jikkata a gobarar fashewar tankar mai a karamar hukumar Ota ta jihar.

KU KARANTA KUMA: Babban magana: An gurfanar da miji kan laifin yiwa matarsa satar kudi

Yayinda yake jajintawa iyalan wadanda suka jikkata a asibiti, Abiodun ya bayyana cewa gwamnonin jihar Legas da Ogun, na shirin kawo karshen asarar rayuka a hanyar. Abiodun ya bada umurnin kaisu asibiti a Legas da Abeokuta kuma ya yi alkawarin dauke nauyin kudin asibitin.

Mun kawo muku rahoton cewa Akalla mutane biyu sun rasa rayukansu, motoci 17 sun kone yayinda watar tanka mai dauke da man fetur ta samu hadari kuma ta kama da wuta a Sango, unguwar Ota, jihar Ogun cikin daren Alhamis, 14 ga Nuwamba, 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel