Buhari ya aika sako ga wadanda sakamakon zaben Bayelsa bai yi wa dadi ba

Buhari ya aika sako ga wadanda sakamakon zaben Bayelsa bai yi wa dadi ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya dan takarar jam'iyyar APC, David Lyon murna a kan nasararsa a zaben 16 ga watan Nuwamba da aka yi a jihar Bayelsa.

Buhari, kamar yadda mai bada shawara gareshi na musamman a kan yada labarai ya sanar a sa'o'in farko na ranar Litinin, ya jinjinawa magoya bayan APC da 'yan Najeriya a jihar da suka sauke nauyinsu na 'yan kasa cikin lumana.

Ya nuna rashin jindadinsa a kan rashin rayukan da aka yi a Bayelsa sakamakon zaben. Ya kara da ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasun.

DUBA WANNAN: Yadda a ka bi dare da duhu a ka kwacemin nasarata - Dino Melaye

Buhari ya ce, "Tashin hankula yayin zabe suna nunawa duniya tare da 'ya'yanmu masu zuwa cewa, ba za mu iya zaben shuwagabanni cikin lumana kuma yadda ya dace ba."

Wajen jaddada kokarin jami'an tsaro da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, ya ce sun yi kokari wajen dabbaka doka. Ya kara da cewa, abin rashin jindadi ne har da aka samu siyen kuri'u daga 'yan siyasa yayin zaben.

Ya ce, a shirye yake don yin aiki da zababben gwamnan don inganta rayukan jama'ar jihar Bayelsa, yayin tabbatar da tsaron rayuka da kadarorin 'yan jihar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga wadanda basu amince da sakamakon zaben ba, da su garzaya kotu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel