Abubuwa 6 da yakamata a sani game da gwamnan jihar Kogi da ya zarce

Abubuwa 6 da yakamata a sani game da gwamnan jihar Kogi da ya zarce

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan jihar da a ka yi a ranar Asabar din nan da ta gabata.

Bello ya samu jimillar kuri'u 406,222 inda ya bige abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Injiniya Musa Wada, wanda ya samu jimillar kuri'u 189,704.

Ga abubuwa shida da yakamata a sani game da Bello:

1. Yahaya Adoza Bello shine cikakken sunansa kuma an haifesa a karamar hukumar Okene ta jihar Kogi a ranar 18 ga watan Yuni 1975.

2. Shi ne auta a cikin 'ya'ya shida da Ubangiji ya albarkaci gidansu da su. Ya yi makarantar firamaren gwamnati da ke Agassa a karamar hukumar Okene a 1984.

3. Ya yi makarantar sakandire da ke Agassa-Okene inda ya samu shaidar kammala karatun aji uku. Ya kammala karatunsa na sakandire a makarantar sakandire ta gwamnati da ke Suleja, jihar Neja a shekarar 1994.

DUBA WANNAN: Magudin zabe: An bukaci INEC ta soke zaben jihar Kogi gaba daya

4. Bello ya yi karatun gaba da sakandire a folitaknik din jihar Kaduna a 1995. Ya samu shaidar kammalar digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a 1999.

5. Ya cigaba da karatunsa a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya samu shaidar kammala digirinsa na biyu a fannin kasuwanci a 2002. Ya samu shaidar zama kwararren akanta daga kungiyar kwararrun akanta ta Najeriya a 2004.

6. Bello ya haye karagar mulkin jihar Kogi a 2015 a karkashin jam'iyyar APC bayan da aka maye gurbinsa da Marigayi Abubakar Audu wanda ya lashe zaben amma ya rasu kafin a bayyana sakamakon zaben.

A yau, hukumar zabe mai zaman kanta, ta bayyana Yahaya Bello a wanda ya lashe zaben jihar da ya gabata a ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel