Murnar samun nasara: Jiga jigan gwamnonin APC sun ziyarci shugaba Jonathan a gidansa

Murnar samun nasara: Jiga jigan gwamnonin APC sun ziyarci shugaba Jonathan a gidansa

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya karbi bakoncin gwamnonin jam’iyyar APC guda biyu a gidansa dake garin Otuoke na jahar Bayelsa a ranar Lahadi, 17 ga watan Nuwamba.

Jaridar The Cables ta ruwaito wadannan gwamnoni na jam’iyyar APC da suka kai ma Jonathan ziyara sun hada da gwamnan jahar Jigawa, Abubakar Badaru da gwamnan jahar Kebbi, Atiku Bagudu, sai kuma hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ita Enang.

KU KARANTA: Wasu Malamai 2 sun yi ta maza, sun arce daga hannun barayin mutane da suka yi garkuwa dasu

Murnar samun nasara: Jiga jigan gwamnonin APC sun ziyarci shugaba Jonathan a gidansa
Jonathan
Source: UGC

Tawagar gwamnonin ta samu kyakkyawar tarba daga tsohon shugaban kasa Jonathan da uwargidarsa Dame Patience Jonathan. Gwamna Badaru da Gwamna Bagudu ne jagororin yakin neman zaben jam’iyyar APC a zaben gwamnan jahar.

Idan za’a tuna dan takarar APC a zaben gwamnan Bayelsa, David Lyon ne ya samu nasara, inda ya lashe zabe a kananan hukumomin jahar guda 6 cikin kananan hukumomi 8, yayin da dan takarar PDP Douye Diri ya lashe kananan hukumomi 2 kacal.

Murnar samun nasara: Jiga jigan gwamnonin APC sun ziyarci shugaba Jonathan a gidansa
Jonathan
Source: UGC

Rahotanni sun tabbatar da cewa jama’an kabilar Goodluck Jonathan sun bayyana farin cikinsu ta hanyar rawa da raye raye yayin da aka sanar da jam’iyyar APC ta lashe karamar hukumar Ogbia, wanda it ace karamar hukumar Jonathan.

Jam’iyyar APC ta samu kuri’u 352, 552 yayin da PDP ta samu kuri’I 143,170, wanda hakan ya bambamta jam’iyyun biyu da kuri’u 209,381. Wannan ne karo na farko da jam’iyyar adawa ke samun nasara a zaben gwamnan jahar tun shekarar 1999.

Murnar samun nasara: Jiga jigan gwamnonin APC sun ziyarci shugaba Jonathan a gidansa
Jonathan
Source: UGC

Sai dai dama ba’a hangi tsohon shugaban kasa Jonathan a yayin yakin neman zaben dan takarar gwamnan jahar Bayelsa na jam’iyyar PDP, Duoye Diri.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel