Gwamnatin jihar Legas ta gano Zakin da ake amfani dashi don gadi

Gwamnatin jihar Legas ta gano Zakin da ake amfani dashi don gadi

- Gwamnatin jihar Legas ta bankado wani gida a jihar da ake amfani da Zaki don gadi

- Wani mutum dan asalin kasar India ne ka rainon jinjirin Zakin mai shekaru biyu a duniya

- Gwamnatin jihar ta ce, za a galabaitar da dabbar dajin a yau Litinin inda za a mikasa gidan Zoo

Gwamnatin jihar Legas ta ce ta gano gidan da ake rainon jinjirin Zaki a jihar. Zakin mai shekaru biyu, ana amfani dashi ne don gadi a gidan da ake gano a jihar ta Legas.

A yayin zantawar wakilin jaridar The Punch da shugaban hukumar haraji, muhalli da laifuka na musamman na jihar Legas, Yinka Egbeyemi, yace za a yi amfani da fasahar zamani don galabaitar da jinjirin zakin a ranar Litinin.

DUBA WANNAN: Kogi: Musa Wada ya ce bai aminta da sakamakon zabe ba

Ya ce, gwamnatin jihar Legas din ta gano jinjirin Zakin ne a gida mai lamba 229, titin Muri Okunola a tsibirin Victoria da ke jihar.

Naman dajin an gano cewa, wani dan asalin kasar India ne ke rainonsa. Mazauna yankin ne suka gano hakan tare da kai korafi ga gwamnatin jihar Legas din.

Egbeyemi ya sanar da jaridar Punch cewa, ma'aikatansu na ta kewayen harabar gidan tun a ranar Juma'a. Ya tabbatar da za a galabaitar da dabbar a ranar Litinin inda za a gaggauta kaisa gidan dabbobi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel