2019: INEC ba ta tantance wanda ya kai ga nasara a Kogi ta Yamma ba

2019: INEC ba ta tantance wanda ya kai ga nasara a Kogi ta Yamma ba

Hukumar zabe mai zaman kan ta a Najeriya watau INEC ta tabbatar da cewa ba a samu wanda ya yi nasara a zaben kujerar Majalisar dattawan yankin Kogi ta yamma ba a zaben da ya gabata.

INEC ta bayyana cewa tazarar da ke tsakanin ‘dan takarar APC wanda ya ke kan gaba, Smart Adeyemi, da kuma Sanata mai-ci, Dino Melaye, bai kai yawan kuri’un da aka soke a Mazabar ba.

An soke zabe a akwatuna har 53 da ke cikin rumfunan zabe 20 da ke fadin yankin Yammacin jihar Kogi a zaben karshen makon jiya. Wannan ya sa aka kashe kuri’u 43, 127 inji hukumar INEC.

Smart Adeyemi ya lashe kuri’a 80, 118 ne yayin da Dino Malaye na jam’iyyar hamayya ya tashi da 59, 548. Tazarar da ke tsakanin manyan ‘yan takarar na 20, 570 bai kai 43, 127 da aka soke ba.

Malamin zaben shiyyar, Olayinde Lawal, ya bayyana cewa babu wanda ya yi nasara tukuna domin kuwa doka ba ta bada dama a bayyana wanda ya lashe zabe a irin wannan yanayi ba.

KU KARANTA: An bayyana yawan mutanen da aka kashe a zaben Kogi

Lawal ya ke cewa hukumar INEC za ta sa rana ta musamman da za a karasa gudanar da zaben. Za a sake yin zabe a rumfuna 53 da aka soke kuri’unsu a baya kafin a tsaida wanda ya yi nasara.

Sanata Dino Melaye wanda ya ke wakiltar Mazabar Kogi ta Yamma a majalisar dattawan ya rasa kujerarsa ne bayan kotun sauraron karar zabe da kotun daukaka kara sun rusa zaben da ya lashe.

Tuni ‘dan majalisar ya fito ya na watsi da sakamakon zaben da aka fitar. Dino Melaye ya ce a-ta-fau ba zabe aka yi a jihar Kogi ba inda shi da Wakilin PDP, su ka ki amincewa da sakamakon.

Wasu kungiyoyi da su ka yi aikin sa-ido a lokacin zaben jihar da kuma Sanatan Kogi ta Yamma sun yi Allah-wadai da yadda aka gudanar da zaben inda su ka yi kira da a soke zaben gaba daya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel