Wasu Malamai 2 sun yi ta maza, sun arce daga hannun barayin mutane da suka yi garkuwa dasu

Wasu Malamai 2 sun yi ta maza, sun arce daga hannun barayin mutane da suka yi garkuwa dasu

Wasu malaman makarantun gaba da sakandari guda biyu yan gida daya da wasu miyagu yan bindiga suka yi garkuwa dasu sun tsallake rijiya da baya sun tsere daga hannun barayin mutanen, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito malaman sun hada da Adamu Chonoko dake koyarwa a jami’ar Ahmadu Bello da Umar Chonoko dake koyarwa a kwalejin kimiyya da fasaha na gwamnatin tarayya dake garin Kaduna, sun tsere ne bayan kwashe kwanaki 10 a hannun miyagun

KU KARANTA: Mataimakin gwamnan Legas ya jefa matafiya cikin rudani a cikin jirgin sama

Kaakakin kungiyar al’ummar jahar Kebbi mazauna garin Kaduna, kuma garkuwan Wakilin Sarkin Zuru a Kaduna, Garba Muhammad ne ya tabbatar da haka ga manema labaru a ranar Lahadi, 17 ga watan Nuwamba.

“Yan gida daya kuma yan asalin jahar Kebbi sun tsere ne daga hannun masu garkuwa, kuma sun isa fadar wakilin Sarkin Zurun Kaduna da misalin karfe 11:51 na safe, wakilin Sarkin Zuru da kansa ya tarbesu. Mun gode ma Allah da Ya kubutar dasu.

“Miyagun sun kama Umar ne yayin da ya tafi ya kai musu babur da kudi N2m a matsayin kudin fansar yayansa Adamu da suka kama, daga nan suka sake neman a basu naira miliyan 5, nan ma aka kai musu cikon naira miliyan 3, sai kuma suka sake neman naira miliyan 10, daga nan muka gaza, kwatsam da safen nan sai gasu sun taho fada tare da taimakon jami’an tsaro.

“Mun gode ma kafafen watsa labaru, jami’an tsaro da duk wadanda suka taimaka wajen yin addu’ar Allah Ya kubutar da mutanen.” Inji shi.

Shi ma nasa bangaren, kaakakin rundunar Yansandan jahar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya tabbatar da bayyanar malaman, inda yace sun samu labarin tserewarsu daga hannun masu garkuwa, kuma a madadin kwamishinan Yansandan Kaduna, Ali Janga, yana tayasu murna.

Daga karshe yace rundunarsu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare dukiya da rayukan jama’an Kaduna, don haka ya nemi jama’a su cigaba da baiwa jami’an tsaro hadin kai da goyon baya, tare da shayar dasu bayanan sirri da zasu taimaka musu a aikinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel