Magudin zabe: An bukaci INEC ta soke zaben jihar Kogi gaba daya

Magudin zabe: An bukaci INEC ta soke zaben jihar Kogi gaba daya

Dakin lura da zabe, karkashin kungiyar Nigerian Civil Society ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta da ta soke zaben jihar Kogi da aka yi a ranar Asabar. Ta yi wannan kiran ne sakamakon hargitsi da siyan kuri'u da ya cika zaben ranar Asabar din da aka yi a jihar.

An yi zaben gwamnan ne a fadin jihar,amma an sake zaben kujerar sanata mai wakiltar yankin Kogi ta yamma.

Masu lura da zaben sun ce, zaben jihar Kogin ya bayyana babban lalacewa da koma baya ga damokaradiyyar Najeriya.

Mashiryin taron kungiyar, Clement Nwankwo, ya sanar da matsayar kungiyar ne a taron manema labarai a garin Abuja a ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: Kogi: Musa Wada ya ce bai aminta da sakamakon zabe ba

Kamar yadda ya ce, in har aka bar wannan zaben a haka, zaben 2023 da na jihar Ondo da za a yi shekara mai zuwa zai kasanace kare-jini, biri-jini.

Kungiyar na daga cikin tantantattun masu lura da zaben.

Jaridar Premium Times ta ruwaito yadda zaben jihar Kogi ya fara da rashin kai kayayyakin zabe da wuri, tashin hankali da tsorata masu kada kuri'a. Amma kuma an samu zaben gaskiya kuma cikin lumana a wasu sassa na jihar.

'Yan takara 24 ne suka fito don neman kujerar gwamnan jihar. Duk da mutane 1,646,350 ne suka yi rijistar katin zabe a jihar, an samu 1,485,828 ne suka karba katikan zabensu. Hakan na nuna su kadai ne zasu yi zabe a kananan hukumomi 21 na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel