Mayakan Boko Haram a kan rakuma sun kai farmaki jahar Adamawa, sun kashe 6

Mayakan Boko Haram a kan rakuma sun kai farmaki jahar Adamawa, sun kashe 6

Wasu gungun mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram sun kai wani samame haye a kan rakuma a wani kauye dake cikin jahar Adamawa, inda suka kashe mutane 6 dake aikin tabbatar da tsaro a yankin, watau ‘yan sa kai’ ko kuma ‘Civilian JTF’.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito yan ta’addan sun kaddamar da harin ne a kauyen Aljannaru dake kan iyakar jahar Borno da jahar Adamawa da sanyin safiyar Lahadi, 17 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Mataimakin gwamnan Legas ya jefa matafiya cikin rudani a cikin jirgin sama

Wani mazaunin garin mai suna David Yaro ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace: “Yan ta’addan sun shigo garinmu ne kafin sallar Asubah a kan rakuma, da shanu inda suka turasu cikin gonakinmu domin su lalatasu.

“Daga nan sai suka hau saman wani tsauni dake kallon cikin kauyenmu, inda suka bude wuta irin harbin mai kan uwa da wabi, bayan nan sai suka fara bi gida gida suna zakulo mutane, sun kashe adadin mutane 6 dake taimaka mana da tsaro a kauyen.” Inji shi.

Shi ma wata majiya daga jami’an tsaro dake jahar Adamawa, wanda keda masaniya game da lamarin ya tabbatar da aukuwarsa, kuma ya bayyana cewa mayakan na Boko Haram sun yi amfani da manyan makamai na zamani wajen kai wannan hari.

Haka zalika wani jagora daga cikin mafarautan jahar Adamawa, Modibbo Tola ya tabbatar da kisan abokan aikinsu, inda yace: “Tabbas, zan iya tabbatar maka cewa mun yi asarar abokan aikinmu guda shida a yayin harin da yan bindigan suka kai a kan rakuma.

“Amma a yayin da muke jimamin mutuwar abokanmu wanda daga cikinsu har da wani babba daga jahar Gombe, za kuma mu cigaba da taimaka ma jama’an wajen basu tsaro.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel